1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Garkame 'yan jarida a kurkuku: Bincike mai hadari

Fürstenau Marcel SB/MNA
December 14, 2020

Kara garkame 'yan jarida a kurkuku a fadin duniya na kara nuna irin matsi da 'yancin albarkacin baki ke fuskata a cewar rahoton kungiyar kare hakkin 'yan jarida ta duniya, "Reporters Without Borders".

https://p.dw.com/p/3mhtg
Deutschland Symbolbild Pressefreiheit
Hoto: Imago Images/S. Boness

Rahoton wanda aka wallafa a wannan Litinin ya nuna halin tasku da 'yan jarida suka samu kansu a ciki a sassa dabam-dabam na duniya da suka hada da jefawa a gidajen fursuna, garkuwa da su gami da bacewa a wasu lokuta. Kasar Chaina wato Sin ke kan gaba wajen garkame 'yan jarida a duniya yayin da kasashen Ruwanda da Mozambik suka yi kaurin suna a nahiyar Afirka. Zuwa farkon watan Disamba 'yan jarida kusan 390 ke gidan fursuna. Kuma bullar annobar corona tsakanin kasashen duniya ta janya samun karin ta'azzara da 'yan jarida ke fuskanta musamman a nahiyar Afirka kamar yadda Sylvie Ahrens-Urbane ta kungiyar 'yan jarida Reporters Without Borders ta yi karin haske. Karin bayani:Dokar tauye kafofin labarai a Tanzaniya

"Afirka ta bi sahu da tasirin bayan kasashen Asiya da Turai. Amma mun ga kai hari kan fadin 'yancin albarkacin baki ya karu lokacin da ake samun karuwar annobar cutar corona. Akwai kame-kamen 'yan jarida da dama daga ranar 15 ga watan Maris zuwa 15 ga watan Mayu kamar abin da ya faru a irin wannan lokaci a shekarar da ta gabata. Masu aiki a kafofin yada labarai 40 aka kama daga farkon watan Maris zuwa karshen Nowamba saboda sun yi rahoton annobar cutar corona."

Mawallafiya Tsitsi Dangaremba na zana-zangar adawa da kame Hopewell Chin'onos
Mawallafiya Tsitsi Dangaremba na zana-zangar adawa da kame Hopewell Chin'onosHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Mukwazhi

Sannan ta kara da cewa akwai dan jaridar Zimbabuwe, Hopewell Chin'ono wanda aka kama saboda bincike kan jami'an gwamnati kan maganin corona wanda ya kashe kimanin kusan wata biyu yana garkame yayin da hukumomi suna hana ba da belinsa. Kana Sylvie Ahrens-Urbane ta kara ba da misali da abin da ke faruwa a kasar Ruwanda:

"Akwai dan jaridan da ke hannu saboda zargin rashin mutunta ka'idojin coronavirus. Wannan dan jarida na Ruwanda mai suna Dieudonné Niyonsenga daraktan wata tashar talabijin kan intanet mai suna "Ishema". An kama shi a watan Afrilu. Yana rahoto kan yadda matakan da gwamnati ta dauka ke shafan rayuwar mutane tare da zargin sojoji da take hakkin dan Adam yayin da suke neman tilas a bi matakin."

Ruhollah Zam dan jaridar da aka aiwatar da hukuncin kisa kanshi a Iran a cikin watan Disamban 2020
Ruhollah Zam dan jaridar da aka aiwatar da hukuncin kisa kanshi a Iran a cikin watan Disamban 2020Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Shirband

Kasashen Belarus da Iran suna sahun gaba wajen cin zarafin 'yan jarida, kuma tun bayan sake zaben Shugaba Alexander Lukashenko kan madafun iko a Belarus, da zanga-zangar da ta biyo baya, 'yan jarida suka shiga tasku. Karin bayani:An aiwatar da kisa kan dan jarida a Iran

Kana ana samun bacewar 'yan jarida a wasu sassa kamar yadda Sylvie Ahrens-Urbane ta kungiyar 'yan jarida Reporters Without Borders ke cewa.

"A wannan shekara 'yan jarida hudu suka bace, biyu daga ciki a yankin Kudu da Sahara na Afirka. Wani dan jarida daga Mozambik ya bace. Sannan akwai daga Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Zuwa ranar daya ga watan Disamba babu wani bayani a kansu ko wanda ya dauke su, ko kuma suna raye a ina."

Akwai dai 'yan jarida 54 da yanzu haka ake garkuwa da su a kasashen da ake yakin basasa kamar Siriya da Iraki gami da Yemen.