1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya: Gwamnan Nairobi na fuskantar zargin rashawa

Zainab Mohammed Abubakar
December 9, 2019

A dai dai lokacin da ake bukin ranar yaki da cin hanci da karbar rashawa a duniya, gwamnan Nairobi fadar gwamnatin kasar Kenya Mike Sonko, ya yi watsi da zargin rashawa da ake masa

https://p.dw.com/p/3UVPz
Kenia Mike Mbuvi Sonko Verhaftet
Hoto: Getty Images/AFP

Cikin zargin da ake wa Mike Sonko har da  sama da fadi da dukiyar kasa da karbar rasha da babakere. An dai dauki tsauraran martakai na tsaro a daidai lokacin da gwamnan ya bayyana domin yin ba'asi a gaban kotu a wannan Litinin, biyo bayan kira ga magoya bayansa da su yi bore a harabar kotun.

Kasar Kenya tana daga cikin kasashen da suka shafe shekara da shekaru na gwagwarmaya kan cin hanci da rashawa, sai dai a shekara ta 2018 da ta gabata kididiga ta yi nuni da cewa kasar da ke gabashin Afrika tana matsayi na 144 daga cikin kasashen duniya 180 kan yawan cin hanci da rashawa. 

Kenia Gouverneur Mike Mbuvi Sonko
Gwamna Sonko na tattaunawa da lauyoyinsaHoto: DW/S. Wasilwa

Yayin zaman kotun an karfafa matakan tsaro lokacin da gwamna Mike Sonko na Nairobi ya bayyana domin amsa tuhumar zargin cin hanci da rashwa a wannan Litinin, inda ya alkawarin zai kare kansa domin ganin an wanke shi daga hukumar da yake zargin yarfen siyasa.

A zaman kotun dai masu gabatar da kara biyar ne suka wakilici gwamnatin kasar Kenya yayin zaman a birnin Nairobi fadar gwamnatin kasar kana kuma tawagar da suka wakilici gwamnan Mike Sonko karkashin jagorancin Harrison Kinyanjui inda ya ce babu wani shaida da aka kawo kotun yana mai cewa.

"Inda kuka dubi shaida aka kawo Kotu bawani shaida gani da ido bane, saboda bani yakamata ace na tofa albarkan baki ba kan wannan batu."

Kenia Senator Mike Sonko
Mike Sonko ya na hira da 'yan jaridaHoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Kafin a gurfanar da Gwamna Mike Sonko a gaban kotu jami'an soji sun kamashi na tsawon sa'o'i 11 karkashin matakan tsaro abun da Lauyan mai kare shi Kinyanjui ya bayyana dashi a matsayin wasa kwaikoyo na fina-finan kasashen ketere.

"Yakamata ku barni nayi ta dariya saboda a wasu lokuta wasan kwaiwayon siyasa ake amfani da shi a gwamnati. Babu dalilin amfani da duk karfin gwamnati domin kama gwamna wanda ko yaushe aka san inda yake wannan abin da ya faru tsararre ne kawai."

A iya kokarin da tasher dw tayi na magana da masu gabatar da kara na gwamnati ya ci tura saboda duk kira da akayi masa sai yace a'a kokuma ya gaji ko yana aiki.