Nijar: Ma'aikatan Orano cikin kunci
December 24, 2024Talla
Duk da alkawuran da kamfanin na Faransa ORANO ya yi musu na biyan su wasu 'yan kudade bayan rufe reshen kamfanin na Cominak har yanzu babu wani abin da aka yi musu.
Gidaje da dama da kamfanin ya gina wa ma'akatan tuni aka fara rushesu tare da katse wutar lantarki. A yau suna yin rayuwa cikin wani mawuyacin hali, ba albasi ba wurin zama abin da ya sa suka fara yin korafi. Daga kasa za a iya sauraron sauti.