1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin ta'addanci a jirgin kasa a Jamus

Sulaiman Babayo/ASJuly 19, 2016

Mahukuntan kasar Jamus sun tabbatar da mutuwar wani mahari da ya kai hari da gatari kan fasinojoji a tashar jiragen kasa da ke Jihar Bavaria a kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/1JRUO
Schwerverletzte bei Attacke in Zug bei Würzburg
Hoto: picture-alliance/dpa/K.-J. Hildenbrand

Wannan matashi ya kasance dan shekaru 17 daga kasar Afghanistan wanda ya ke neman mafaka a kasar ta Jamus amma ya rasa ransa lokacin da ya kai hari da gatari kan jirgin kasa a Wuerzburg kusa da wata tasha cikin daren ranar Litinin din da ta gabata. Jirgin dai na dauke ne da fasinjoji kimanin 30 lokacin da ya kai harin.

Ministan cikin gida na Jihar Bavaria da lamarin ya faru Joachim Herrmann "da yammacin tsakanin karfe 9 zuwa 9 da minti 15 maharin ya dan shekaru 17 ya kaddamar da harin kan fasinjoji ya na dauke da gatari a cikin tashar jiragen kasa. Hari ne mai muni. A cikin wadanda abun ya shafa akwai wasu iyalai 'yan China da suke yawan bude ido."

Bayern Attacke in Regionalzug bei Würzburg-Heidingsfeld Blutfleck
Maharin ya jikkata mutane da dama bayan da afka musu da wani gatari da ke hannunsaHoto: picture-alliance/dpa/K. Hildenbrand

Herrmann ya kuma shaida wa tashar talabijin cewa masu bincike sun gano wata tuta da aka zana da hannu a gidan maharin da ke nuna ya rungumi matsananci ra'ayin addinin Islama irin na kungiyar IS mai ikirarin neman kafa daular Islama. Sannan 'yan sanda suna bincike kan wasu kalamai na addinin Islama da wasu shaidu suka ce maharin ya furta lokacin ya da kai harin da gatari.

Deutschland Attacke in Regionalzug bei Würzburg
'Yansanda na cigaba da gudanar da bincike kan wannan harin da matashin ya kai bayan da aka gano kamar yana da alaka da ISHoto: picture-alliance/dpa/K. J. Hildenbrand

Sakataren ma'ikatar harkokin cikin gida na jihar ta Bavaria Gerhard Eck mai kula da gine-gine gami da harkokin sufuri ya yi karin haske bisa mutuwar maharin dan kasar Afghanistan inda ya ce "lokacin da wanda ake zargi ya tsere zuwa yankin gabar ruwan Main, babu wata hanya da ta rage masa sai ya wuya kan 'yan sanda da gatarin da ke hannunsa da wuka. 'Yan sanda ba su da wani zabi da ya rage musu sai kare kai a karshe bayan harbe-harbe an bindige maharin."