Yarjejeniyar Oslo ta gaza samar da zaman lafiya
September 13, 2018Shugaban Falasdinawa Yasser Arafat na wancan lokacin da marigayi Firaminista Yitzhak Rabin na Isra'ila, su ne suka sa hannu kan yarjejeniyar karkashin sa idon tsohon Shugaban Amirka Bill Clinton. Yarjejeniyar zaman lafiyan da aka cimma, ga wadanda suka taka rawa aka samu tattabar da ita, suna cewa inda an aiwatar da ita kawo yanzu da an kawo karshen zubar da jini a yankin. Ga al'ummar kasar ta Norway kuwa har yanzu suna alfahari da wannan rawar da kasarsu ta taka a wancan lokacin, inda har ta kai ga amincewa da yarjejeniya kan rikici mafi sarkakiya a duniya.
A wancan lokacin dai an amince da cewar Isra'ila da Falasdinawa za su yi aiki tare don bai wa Falasdinawa 'yancinsu, a bisa abin da Majalisar Dinkin Duniya ta yarda, wato gabashin Kudus ya kasance babban birnin Falasdinawa, yayin da za a shata kan iyakar kasashen biyu.
Kafin wannan lokacin dai hukumomin Isra'ila sun dauki shugaban Falasdinawa a matsayin dan ta'adda.
Sai dai sannu a hankali wannan yarjejeniyar ta ruguje, musamman bayan da aka hallaka Firaminista Yitzhak Rabin na Isra'ila wanda ya sa hannu kan yarjejeniyar. A yanzu wannan yarjejeniyar ta Oslo ta zama sai dai a takarda, domin Isra'ila sai kara ba da dokar rusa kauyukan Falasdinawa take yi, inda kuma ita kanta kasar Amirka mai shiga tsakani, a karshin gwamnatin Trump ta fito a fili ta nuna cewa ita ta dauki bangarei, kuma har ta hana kudin tallafin da ake ba wa Falasdinawa, ta dawo da ofishin jakadancinta Birnin Kudus, kuma ta kori wakilan Falasdinawa a kasar Amirka. Baya-bayan nan Donald Trump ya ce kawai a hade yankin Falasdinawa da Jordan su zama kasa daya.