Bennett ya zama firaministan Isra'ila
June 14, 2021Tuni dai kasashen duniya gami da al'ummar Isra'ilan, suka fara mayar da martani game da sabon firaministan da ke da tsattsauran ra'ayi. Daruruwan al'umma ne ke bikin kawo karshen mulkin Benjamin Netanyahu da ke zaman tsohon firaminstan Isra'ilan, tare da yin maraba da Naftali Bennett. Mai shekaru 49 dan jam'iyyar Yamina mai ra'ayin rikau, ya Benjamin Netanyahukasance tsohon kwamandan sojojin kasar kana guda daga cikin na hannun daman Benjamin Netanyahu kuma mai adawa da kafa kasar Falasdinu.
Karin Bayani: Shirin kafa gwamnatin hadaka a Isra'ila
Firaminista Bennett zai kasance a kan ragamar mulki har nan da watan Satumbar shekara ta 2023, kafin ya mika mulki ga wata jam'iyya a karkashin tsarin karba-karba da kasar ke kai: "Sabuwar rayuwa ta fara a wannan kasa tamu, za mu yi aiki tukuru domin tabbatar da hadin kan al'umma. Mun san cewa yanzu idanuwan kowa na kanmu, za mu yi aiki da kowane bangare domin kawo karshen barakar da muka samu tsawon lokaci."
Da alama wannan shan kaye da tsohon firaministan Isra'ilan Benjamin Netnayahu da jam'iyyarsa ta Likud suka yi bai yi musu dadi ba, duk kuwa da cewar sun kwashe shekaru suna jan ragamar mulki. A jawabin da ya yi wa majalisa a lokacin da ake dakon sakamako, Netanyahu ya sa alwashin zama dan adawa da zai mayar da mulki ga jam'iyyarsa: "Idan har kaddararmu ce mu koma 'yan adawa, to kuwa za mu yi da alfahari har sai mun karbe iko daga hannun wannan gurguwara gwamnatin da aka kafa domin mayar da ikon kasarmu yadda muka saba."
Karin Bayani: Firaminista na shirin kafa gwamnati a Isra'ila
Su ma adai Falasdinawa da ke da tsamin dangantaka tsakaninsu da Isra'ila na tofa albarkacin bakinsu game da wannan sabuwar gwamnati. Mai magana da yawun kungiyar Hamas Fawzi Barhoum na ganin da waccan gwamnatin da wannan duk dodo daya suke wa tsafi: "Duk wata hanya da wannan sabuwar gwamnati za ta dauka ba zai canza yadda muke kallonsu a matsayin masu karbe mana matsugunanmu ba, kuma za mu ci gaba da bujire musu. Da farko za mu duba kamun ludayinsu domin shi ne zai tabbatar da yadda za mu tafiyar da su, za mu ci gaba da kare al'ummarmu da ma Masallacinmu da ke da matukar muhimmanci."Tuni shugabannin kasashen duniya suka fara taya sabon firaministan murna. Shugaban Amirka Joe Biden ya taya sabon shi murna ya kuma sake jaddada ci gaban alakar kasarsa da Is'ila, inda ya nanata cewar ba ta da kawar da ta wuce ta. Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a sakon taya murnar da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce Jamus da Isra'ila na da wata kyakkyawar alaka da take fatan ci gabanta a wannan sabuwar gwamnatin. Firaministan Birtaniya Boris Johnson da Kanada, na daga cikin wadanda suka isar da sakonninsu. Sai dai Justin Trudeau na Kanada, na fatan ganin an samu fahimtar juna tsakanin Isra'ilan da Falasdinu.