1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSiriya

Jagoran Siriya ya gana a karon farko da jami'an Amurka

December 21, 2024

Amurka ta sanar da janye tukwicin da ta saka a baya ga duk wanda ya kamo mata Hayat Tahrir al-Sham, sabon shugaban Siriya bayan ganawar farko da jami'an diflomasiyyanta suka yi da shi tun bayan kifar da al-Assad.

https://p.dw.com/p/4oRvo
Syrien Bürgerkrieg HTS-Führer Abu Mohammed al-Jolani
Hoto: OMAR HAJ KADOUR/AFP/Getty Images

Da yammacin Juma'ar nan sabbin jagorin Siriya da suka kifar da Bashar al-Assad bayan share shekaru 13 suna kai ruwa rana da shi sun ce a shirye suke su ba da gudummowa wajen dawo da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya tare kuma da buda kofofin kasar ga kasashe masu manufofin ci gaba a yankin.

Sabbin mahukuntan Siriya sun bayyana hakan a cikin sanarwar da suka fidda bayan kammala ganawar farko tsakannin shugaban wuccin gadi Hayat Tahrir al-Sham da wata tawagar manzannin Amurka da ta yi tattaki har zuwa birnin Damascus.

Karin bayani: Jami'an diplomasiyyar Amurka na ziyara a Siriya

Jim kadan bayan ganawar, ofishin jakadancin Amurka ya fidda sanarwar cewa Washington ta janye tukwicin da ta saka a baya ga duk wanda ya kamo mata sabon shugaban na Siriya Hayat Tahrir al-Sham a lokacin da ya ke gwagwarma a kungiyar 'yan ta'adda ta IS.

Sanarwar ta kuma bukaci sabbin jagororin da su gudanar da mulkin rikon kwarya cikin gaskiya da adalci wanda ya dace da 'yan Siriya tare kuma da kiyaye tsokanar makwabta.

Wannan dai na nufin cewa sabbin jagororin Siriyar na wucin gadi sun fara samun karbuwa a idonuwan manyan kasashen duniya da a baya ke zaman doya da manya ja da Shugaba al-Assad da aka hambarar.