1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jami'an diplomasiyyar Amurka na ziyara a Siriya

Binta Aliyu Zurmi
December 20, 2024

Manyan jami'an diplomasiyyar Amurka na ziyarar farko a kasar Siriya tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

https://p.dw.com/p/4oOQ3
Jordanien | Antony Blinken
Hoto: Andrew Caballero-Reynolds/AP Photo/picture alliance

Jami'an da tuni suka isa birnin Damascus za su tattauna da shugababbin kungiyar Hayat Tahrir al-Sham da ke jan ragamar kasar a yanzu.

Daga cikin manyan batutuwan da tattaunawar ta su za ta mayar da hankali akwai batun dan jaridar Amurka Austin Tice da ya yi batar dabo a kasar tun a shekarar 2012.

Kazalika batu na kare hakkin tsirarun al'ummar Siriya da na ayyukan 'yan ta'adda gami da batu na makamai masu guba, gwamnatin Biden ta ce ka iya kawo cikas ga taimakonta ga wannan gwamnati.

Tawagar ta Amurka da ke ziyarar farko a hukumance tun bayan rufe ofishin jakadancinta a kasar a shekarar 2012, za ta kuma tattauna da kungiyoyin al'umma a yankuna daban-daban na kasar, domin samar da kyakyawar makoma ga al'umma bayan Assad.

 

Karin Bayani:Bukatar gudanar da sahihin zabe a Siriya