William Ruto: Ba daukar fansa a siyasar Kenya
August 18, 2022Hukumar zaben kasar ta Kenya kdai ce zababben shugaba William Ruto ya lashe zaben shugaban kasa da kashi 50,49 cikin 100 yayin babban abokin hamayyarsa Raila Odinga ya samus kaso 48 cikin 100 na kuru'un da aka kada. A ranar Litinin da aka bayyana sakamakon zaben, an samu barkewar zanga-zanga a yankin Kisumu da ke arewacin kasar da kuma yankunan da ke kusa da Nairobi, babban birnin kasar bayan da magoya bayan tsohon firaminista Raila Odinga suka yi zargin cewar an tafka magudi.
To sai dai a jawabin da ya yi bayan samun nasara William Ruto ya yi kira ga al'ummr kasar da ta hada kai don ci gaban kasar tare da yafe wa juna irin abubuwan da suka faru a baya.
"Ina so na yi wa daukacin al'ummar Kenya alkawari wanda suka zabe mu da ma wanda ba su zabe mu ba cewa wannan ita ce gwamnatinsu. Babu daukar fansa, babu waiwaiye, muna duban gaba, ina sane da cewa kasarmu tana kan wani mataki da muke bukatar gundunmowar kowa" in ji Ruto
Kawo yanzu dai tsohon firaminista Odinga mai shekaru 77 da ya sha kaye, ya yi watsi da sakamakon zaben. Kusan shekaru 20 ya kwashe yana karawa a zaben shugaban kasar ba tare da samun nasara ba. Amma an shirya a Talatar nan jam'iyyarsa za ta sake kidayar kuri'un domin tantance gaskiyar sakamakon zaben. Jam'iyyar na da makwannin biyu a gabanta domin kalubalantar sakamakon zaben a gaban kotu.
A zabukan Kenya da suka gabata kusan mutane 1000 suka mutu biyo bayan rikicin zaben yayin da wasu dubban mutane suka kaurace wa matsugunansu. Zababben shugaba William Ruto na da jan aiki a gabansa na sake hada kawunan al'ummar kasar mai yawan mutane miliyan 65, kasar da ke cikin wani hali na koma bayan tattalin arziki, da rashin aikin yi, ga talauci sannan ga cin hancin da karbar rashawa da suka yi wa kasar katutu.
Yanzu haka akwai zarge-zarge da ake yi kan William Ruto na kwace filayen jama'a da kuma wasu zarge-zarge na cin hanci amma duk da haka wasu 'yan kasar na fatan zai iya magance kalubalen da suke fuskanta.
Kenyar dai ita ce kasa mafi karfin tattali arziki a yankin gabashin Afirka amma barkewar annobar corona da yakin Ukraine sun janyo dagulewar al'amura ga kasar da ke dogoro da sana'ar noma da kiwo.