Kalubalen sabuwar gwamnatin Mozambik
October 31, 2014A ranar 15 ga watan Oktoba ne dai aka zabi Filipe Nyusi a matsayin sabon shugaban kasar ta Mozambik biyo bayan lashe kuri'un da aka kada a babban zaben kasar da sama da kaso 50. A yanzu haka kowa ya zubawa Nyusi idanu ne domin ganin yadda zai gudanar da mulkinsa da ke cike da kalubale mai yawa. Tun bayan da kasar Mozambik ta samu 'yancin kanta daga kasar Potugal a shekara ta 1975 jam'iyyar Frelimo ce ke mulki a kasar sai dai wannan ne karon farko da aka zabi shugaba a karkashinta daga arewacin kasar. hin ko me al'ummar kasar ta Mozambik ke bukata daga Filipe Nyusi a yanzu da aka zabe shi a matsayin sabon shugaban kasa? Ga abin da wani ke cewa..
Abun da al'umma ke bukata
"Abun da talakan Mozambik ke bukata kuma muke dako shine ai aiki domin ci gabanmu. Abun da muka fi bukata a yanzu shine tsaftataccen ruwan sha da kuma inganta muhalli a jihohinmu dama kasa baki daya."
Filipe Nyusi dai shine tsohon ministan tsaron Mozambik kafin jam'iyyar tasa ta Frelimo ta zabeshi a matsayin dan takarata na shugabancin kasar a ranar daya ga watan Maris na wannan shekara da muke ciki. An haifi Filipe Nyusi a garin Namau kuma iyayensa sun kasance masu yin kamfe na tabbatar da samun 'yancin kan Mozambik daga kasar Potugal a wancan lokaci karkashin jam'iyyar Frelimo. Filipe Nyusi ya yi karatunsa a makwabciyar kasa Tanzaniya kafin daga bisani ya samu horo a aikin sojo. Ya kuma yi digiri a fannin Injiniya. Bayan ya kawashe shekaru yana aiki ba tare da shiga harkokin siyasa ba, shugaba mai barin gado Armando Guebuza ya nada shi a matssayin ministan tsaro a shekara ta 2008, kafin daga bisani.
Shakku kan alkawuran da ya dauka
A yayin gangamin yakin neman zabensa Nyusi ya yi alkwura da dama ga al'ummar kasar, inda ya yi alkawarin dorawa daga inda wanda ya gada Armando Guebuza ya tsaya musamman wajen tabbatar da dorewar mulkin dimokaradiyya da ma ci gaban tattalin arziki. Sai dai wasu 'yan kasar na ganinsa a matsayin mutum mai kabilanci ta yadda suke da shakku kan abubuwan da ya alkawarta musu kamar yadda wanan ke cewa....
"A baya Nyusi ya nuna cewa zai gudanar da aikinsa ba tare da nuna kabilanci ba, sai dai ni bani da yakini a kan hakan. Kawai zai ci gaba ne da yin shugabanci irin na tsohon shugaba Guebuza ne. Ya kuma nuna kansa a matsayin wanda ke wakiltar wata kabila guda ba wai kabilun kasar baki daya ba. Ina ganin ra'ayinsa ya sha ban-ban da na Shugaba guebuza."
Zaben na Mozambik dai an gudanar da shi ne bayan da aka cimma yarjejeniya tsakanin gwamnati karkashin jam'iyya mai mulki ta Frelimo da kuma ta sake lashe zaben da kuma babbar jam'iyyar adawa ta Renamo wanda ya kawo karshen rikicin da kasar ta kwashe shekaru a ciki, kuma ya bude sabon babin dimokaradiyya a kasar.