1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen Larabawa sun katse hulda da Katar

Salissou Boukari
June 8, 2017

Kasashen Saudiyya da Masar da Baharain da kuma Daular Larabawa sun sanar da katse huldar diplomasiyyarsu da kasar Katar a bisa zarginta da tallafa wa kungiyoyin 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/2eKF5
Saudi Arabien Gespräche 136th Golf Kooperationsrat GCC Themen Öl Syrien Yemen Salman bin Abdulaziz Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum
Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya, da Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum mataimakin shugaban Daular Larabawa.Hoto: Getty Images/AFP/Fayez Nureldine

Matakin da manyan kasashen Larabawa suka dauka na mai da kasar Katar saniyar ware kan zarginta da goyan bayan ta'addanci na kara jefa al'ummar Larabawan cikin halin rashin tabbas.