1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron yaki da ta'addanci a Kenya

Michael Oti ZAK/LMJ
July 11, 2019

Birnin Mombasa na kasar Kenya wanda a baya ya kasance gurin zuwan masu yawon bude idanu daga kowanne bangare na dunya, a yanzu ya zama gurin da baki ke fargabar ziyara saboda matsalar tsaro.

https://p.dw.com/p/3LwPL
Kenia Angriff auf Hotel in Nairobi
Hare-haren ta'addanci a Kenya na sanya fargaba ga masu yawon bude idanuHoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Tun bayan tsanantar ayyukan ta'addanci a birnin Mombasa na kasar Kenya sakamakon yadda kungiyar Al-shabaab da ke da sansani a kasar Somaliya ke yi wa matasa romon bakan biyan su kudade masu yawa idan suka shiga kungiyar, mahukuntan kasar Kenyan da taimakon Majalisar Dinkin Duniya suka dukufa domin gano yadda yankin na Mombasa ya rikide zuwa sansanin kyankyasar 'yan ta'adda. An dai gano cewar wasu malaman addini a yankin ne ke da alhakin sauyawa matasa tunani tare da ingiza su shiga ayyukan ta'addanci. Malaman dai kan cusa tsattsauran ra'ayin addini ga matasan ta hanyar wa'azin da suke yi musu a guraren koyarwa. Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres na daga cikin wadanda suka yi jawabi a taron kamar haka, inda ya ce:

Kasashen Afirka sun yi kakori sosai wajen kaddamar da shirin Majalisar Dinkin Duniya na yaki da ta'addanci da kuma yada tsattsauran ra'ayin addini a ciki da wajen kasashen, yanzu kuma lokaci ya yi da kasashen Turai za su bayar da gudummawar kudade da kayan aiki domin yakar ta'addancin da 'yan Afirkan za su jagoranta kuma su gudanar, amma fa tilas a kula da kare hakkin dan Adam da bin doka da oda da kuma  la'akari da jinsi.

Kasar Kenyan dai ta jima tana dora alhakin ayyukan ta'addancin da ya yi kama wuri zauna a kasar, kan kungiyar al-Qa'ida mai alaka da al-Shabaab din da kuma masu nuna tausayawa ga wadannan kungiyoyi daga cikin al'ummar kasar, tun bayan faruwar wasu hare-hare a biranen Nairobi da Mombasa da kuma arewacin kasarkasar ta Kenya.