Kisan kashoggi ya bar baya da kura
October 25, 2018Talla
Hukumomin kasar Saudiyya sun ce bincike da ake gudanarwa game da kisan dan jaridar nan Jamal Kashoggi wanda ya mutu a ofishin jakadancin Saudiyya a Turkiyya zai bankado gaskiyar al'amuran da suka faru.
Ministan harkokin wajen Saudiyyar Adel al Jubeir wanda ya baiyana hakan ya jaddada kudirin gwamnatin Saudiyya na tabbatar da cikakken bincike da zai baiyana gaskiya.
Shi ma yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya yi alkawarin hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu a kisan dan jaridar.