Kasashen yammacin Afirka na neman yin kudin bai daya
June 28, 2019Talla
A taron da zai gudana a ranar (29-06-19) na shugabannin kasashe na yankin yammacin Afirka a Abuja tarrayar Najeriya za a san shawarar karshe da kasashen suka yanki. Sai dai kafin taron tun farko Najeriya ta soma nuna yin dari-dari da shirin kudin bai dayan. Duk da cewar dai tun daga shekara ta 2000 ne dai kasashen suka fara tunani na kirkiro kudi na bai daya a tsakanin al’ummar yankin yammacin Afirka kusan miliyan 300, har ya zuwa yanzu dai siyasar gado da kila tsoron-tsoro dai na ci gaba da jawo kila wakala game da kudin na bai daya a tsakanin kasashen .