Sudan:An koma tattaunawa neman sulhu
June 12, 2019Talla
Banagrorin biyu sun lamunta da daukar matakan samar da amintar juna tsakaninsu don haka a yanzu majalisar soji ta lamunta da sakin dukkanin firsinonin siyasa da masu zanga-zangar da aka tsare. A yayin da su kuma masu fafutukar neman sauyi ke amincewa da jingine boren gama garin da suke yi, kakakin tawagar Kasar Habasha, Mahmud Darir wanda ya jagoranci tattaunwar ya ce ana kan hanyar samun masalha tsakanin bangarorin biyu. A hanu guda kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta nuna damuwarta kan sake bullar mayakan Janjaweed a yankin Darfur, yadda suka harbe kimanin mutane goma da kone gidaje da shagunan mutanan da suka shiga boren gama gari a yankin.