Kotu ta yanke wa Habre hukunci rai da rai
May 30, 2016Kotun musamman ta hukunta manyan lafukan yaki ta Afrika mai cibiyarta a birnin Dakar na kasar Senegal ta yanke hukuncin zaman kason rai da rai ga tsohon shugaban mulkin kama karyar kasar Chadi Hissene Habre, bayan da ta same shi da aikata laifuka da dama da suka hada da na hallaka jama'a dama fyade a kasarsa lokacin da ya ke mulki. Kotun ta bayyana wannan hukunci ne lokacin wani zama da ta gudanar a wannan Litinin.
Jama'a dai sun hallara a kotun ta birnin Dakar domin jin yadda za ta kaya a game da wannan shari'a mai cike da tarihi. Tarin jami'an tsaro sun ja daga a gaban harabar kotun inda suke bincikar duk mutuman da zai shiga kotun ka dauka tun daga 'yan uwa da aminan arzikin mutanen da suka shigar da karan da magoya bayan Hissene Habre din da 'yan jarida kai har da lauyoyi da kansu sai da aka bincika da nufin tabbatar da tsaro.
An shigo da Hissene Habre a cikin zauren shari'ar ya na mai sanye da tufafi farare kuma ya kasance a nutse. Bayan ya karanto masa jerin laifukan da kotun ta same shi da aikatawa daga karshe alkalin kotun Gustave Kam ya sanar da Hissene Habre da hukuncin zaman kason rai da rai da ya yanke masa. Mutanen da tsohon shugaban ya zalinta da danginsu sun yi ta kururuwa tare da bayyana gamsuwarsu da hukuncin da alkalin ya yanke wa tsohon shugaban Chadin.
To sai dai a daidai lokacin da mutanen da tsohon shugaban ya zalinta ke nuna farin cikinsu abin akasin haka ya ke daga bangaren dangin Hissene Habre din da suka halarci zaman shari'ar. Saissala Habre kani ne ga tsohon shugaban ya kuma ce ''babu shari'a a Afirka, wannan wata rufa-rufa ce kawai aka tsara domin faranta wa wasu da rai dan haka ban yi mamaki ba"
Shi ma wani mai goyan bayan Hissene Habre cikin fushi ya ce "mugun aiki ne kawai na karnukan farautar kasar Faransa, idan ba haka ba ta yaya za a yi wa mutane wannan wasan kwaikwayo. Kuma abin bakin ciki shi ne wannan danyen aiki an yi shi ne a kasar Senegal kasar Cheik Anta Diopp"
Daga nasu bangare kungiyoyin kare hakkin dan Adam na Afirka bayyana wannan hukunci suka yi da cewa wata babbar nasarar ce ga fannin shari'ar Afirka. Aliyu Tinne shi ne shugaban hukumar kare hakkin dan Adam ta kasar Senegal ya kuma ce "da ga yanzu za a iya cewa tarihi ya kafu har abada, domin a duk lokacin da aka aika da wani shugaban kasar Afirka a gaban kotun ICC tamkar wani abin kunya ne ga kotunan Afirka"
Kotun dai ta samu Hissene Habre da aikata laifuka da dama da suka hada da na keta hakkin dan Adam da aikata fyade da bautarwa da karfi da aikata kisa da gangan, da sace mutane, da gana wa mutane azaba dama tsaresu ba a kan ka’ida ba da dai sauransu. Amma kuma ta ce ya na da kwanaki 15 a nan gaba domin daukaka kara idan bai gamsu da hukuncin da ta zartar masa ba.