SiyasaSudan
'Yan gudun hijirar Sudan sun cika Sudan ta Kudu
December 23, 2024Talla
Dubban mutane daga Sudan na shiga kasar wadanda suka ke tserewa zafafan fadan, in ji kungiyar likitocin.A cewar kungiyar, a kowace rana sama da mutane dubu biyar ke tsallaka kan iyaka zuwa Sudan ta Kudu,wadda ita ma ke fama da tashe-tashen hankula na yau da kullum, baya ga iftalin yanayi.Tun daga watan Afrilun na shekara ta 2023, yaki ya barke a kasar Sudan, wanda ya hada da sojoji karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhane, da dakarun Rapid Support Forces (FSR) na tsohon mataimakinsa, Janar Mohamed Hamdane Daglo. Kawo yanzu dubun-dubatar mutane suka mutu, yayin da wasu sama miliyan 11 suka rasa matsugunansu.