Magance kwararar bakin haure na Afirka
September 8, 2015Majalisar Dinkin Duniya ta ce duk wata ana samun bakin haure kimanin 5,000 daga kasar Iritiriya ne ke tserewa daga kasarsu zuwa nahiyar Turai. Wani sabon rahoto da hukumar kare hakkin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ya nunar da cewa mutane na kauracewa kasar ce saboda take hakkin dan Adam da kuma cin zarafin al'umma da mahukuntan kasar ke yi.
Tuni dai kungiyar EU da wasu kasashen Afirka da suka hada da Masar da Habasha da Sudan da Sudan ta Kudu da kuma Iritiya gami da kungiyar kasashen Afirka ta AU suka gama kai don tinkarar wannan matsala. Kasashen da kungiyoyin dai za su fitar da tsarin ne domin magance kwararar bakin hauren zuwa Turai da aka yi wa lakabi da Sudan Process.
To sai dai a daura da wannan daraktar kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch a kasar Beljiyum Lotte Leicht ta ce in har ana kokarin kare mutanen da suke shiga hallaka wajen biyo wa ta teku domin zuwa Turai to kuwa bai kamata a hada karfi da kasashen Sudan da Iritirya da suka yi kaurin suna wajen cin zarafin dan Adam ba, in ko aka yi hakan to ba lallai a kai ga cimma nasarar da aka sanya a gaba ba.
Baya ga wannan masu rajin kare hakkin dan Adam na da ra'ayin cewa daya daga cikin wadanda za a hada kai da su domin magance matsalar bakin hauren wato Shugaba Umar al-Bashir na Sudan na daga cikin wanda kotun hukunta masu aikata laifukan yaki ta kasa da kasa ta ICC ke nema ruwa a jallo bisa zarginsa da aikata kisan kiyashi a yayin rikicin yankin Darfur na Sudan din, wanda shi ma ake ganin zai iya kasance babban kalubale wajen kawar da abubuwan da ke haifar da hijira daga Afirka zuwa Turai.