Tsugune ba ta kare ba a Sudan ta Kudu
August 17, 2015A ranar Litinin wa'adin da hukumar hadin kan kasashen Afirka ta Gabas, wato IGAD ta shimfida ya cika. Idan har shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir da abokin adawarsa, kuma shugaban 'yan tawaye, Riek Machar basu daidaita tsakaninsu ba, abinda kuwa ya gagara. Hakan na nufin kasar tana iya fuskantar takunkumi daga kungiyar.
Duk da mummunan halin da al'ummar Sudan ta Kudu suke ciki, amma akwai alamun gwamnati da 'yan tawayen basa iya daidaitawa da juna yadda za su sami zaman lafiya, inji Peter Schuman, lokacin da yake hira da DW. Ya ce idan har bangarorin biyu sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya sakamakon matsin lamba daga ketare, to kuwa yarjejeniyar ba zata kai ko ina ba, kamar dai ire-irenta da suka sha sanya hannu kansu suna rushewa tun da rikicin kasar ya barke a watan Disamba na shekara ta 2013.
Ya ce" A ra'ayi na kuma a binciken da na yi, na gano cewar shugaba Salva Kiir ko shugaban 'yan tawaye Riek Machar, cikinsu babu wanda yake samun cikakkiyar biyayya daga bangaren mayaka ko bangaren siyasarsa. Shugabannin biyu babu abin da ya dame su da wani batu na zaman lafiya, abin da suka damu dashi kawai shi ne yadda zasu ci gaba da daukar matasa aikin soja, yayin da akwai matsaloli masu tarin yawa a bangaren Salva Kiir.
Kungiyoyi da kasashen duniya, musamman Amirka, suna ci gaba da barazanar dorawa kasar ta Sudan ta Kudu takunkumi. Saboda haka idan aka ci gaba da yaki a kasar, duka bangarorin masu gaba da juna suna iya shiga takunkumin hana su tafiye-tafiye da toshe ma'ajiyar kudadensu a ketare da takunkumin hana su sayen makamai. Duk da haka, Peter Schumann ya ce bai yi imanin barazanar takunkumi zai sanya bangarorin na Sudan ta kudu su kai ga fahimtar juna ba, saboda Salva Kiir da Riek Machar suna ganin irin wannan takunkumi ba zai shafesu kai tsaye ba.
Daya daga cikin matsalolin da ke hana ruwa gudu a kokarin cimma zaman lafiya tsakanin Salva Kiir da Riek Machar shi ne yadda za a raba madafun iko a kasar da sai a shekara ta 2011 ne ta sami cikakken mulkin kanta.
Taron da IGAD ta shirya a yanzu, ana ganin shi ne dama ta karshe domin cimma yarjejeniya mai dorewa a kasar. Cikin masu halartar taron kolin a birnin Addis Ababa, har da shugaba Uhuru Kenyata na Kenya da Yoweri MUseveni na Yuganda. Babban jami'in neman sulhu na IGAD, Seyoum Mesfin wanda ya ce wajibi ne Salva Kiir da Riek Machar su halarci zagayen karshe na taron, muddin ana bukatar cimma zaman lafiya, ya ce ana bukatar mutanen da suke da cikekken izinin sanya hannu kan duk wata yarjejeiya ta zamanlafiya idan ta samu. Peter Schuman ya ce a bayan shugabannin na Sudan ta Kudu ma, sabani tsakanin su kansu shugabannin kasashen IGAD yana cikas a kokarin daidaita rikicin kasar.
Ya ce "Idan aka duba masu neman sulhun, za a ga cewar akwai sabani tsakanin Uganda da sauran masu fafutukar neman sulhun. Saboda haka ne muke ganin cewar a tsakanin su kansu masu neman sulhun, akwai gagarumin sabanin da ke hana ruwa gudu a dukkanin bangarori. Saboda haka ne duk abin da suka tsaya kansa, idan ma sun kai ga hakan, ba zai dade ba, ba kuma zai kawo sulhun matsalar ba.
A halin da ake ciki, ana kara samun 'yan Sudan ta Kudu da ke kaurace wa kasarsu zuwa wasu kasashe makwabta domin tsira daga yakin da yaki ci, yaki cinyewa a kasar. Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya zuwa yanzu 'yan Sudan ta Kudu akalla 600.000 ne suke neman mafaka a kasashe makwabta, musamman a Habasha da Kenya da Uganda da Sudan, yayin da wasu mutane miliyan daya da rabi suke zaman hijira a cikiink asar ta Sudan ta Kudu.