1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani bayan hambarar da al-Bashir na Sudan

Gazali Abdou Tasawa YB
April 11, 2019

Amirka da Faransa da Jamus da Birtaniya da Beljiyam da Poland daga nasu bangare sun kira zuwa taron gaggawa na kwamitin tsaro na MDD domin nazarin halin da ake ciki a kasar ta Sudan.

https://p.dw.com/p/3GcDn
Sudan Proteste gegen Präsident Omar Al-Bashir in Khartoum
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wasu 'Yan kasar ta Sudan sun ci gaba da zanga-zanga a gaban babbar hedikwatar sojin kasar ta Sudan da ke a birnin Khartoum jim kadan bayan da sojojin kasar a karkashin jagorancin Awad Ahmed Benawf, ministan tsaro kana mataimakin tsohon shugaban kasa Al-Bashir suka karbe mulki tare da sanar da kafa wata hukumar mulkin soja wacce za ta jagoranci mulkin rikowan kwarya na tsawon shekaru biyu kafin shirya zabe matakin da masu-zanga-zangar suka bayyana a matsayin wata yaudarar da ba za su taba amincewa da ita ba.

Sudan, Demonstration
Hoto: picture-alliance

To sai dai a daidai lokacin da wasu 'yan kasar ta Sudan suka shiga takun saka da sabuwar hukumar mulkin sojin kasar kasashen duniya sun soma bayyana matsayinsu a kan halin da ake ciki a kasar ta Sudan da ma sanarwar sojojin. Daga nata bangare dai kasar Rasha kiran zaman lafiya ta yi ga kasar.

Ita ma dai kasar Masar ta bakin ministan harakokin wajenta cewa ta yi imani da al'ummar Sudan da sojojinta za su iya samun fahimtar juna a bayan mulkin al-Bashir don tabbatar da zaman lafiya da wadata da samar da ci-gaba mai dorewa a kasar kana ta yi kira ga kasashen duniya da su kawo goyan bayansu ga al'ummar kasar ta Sudan. Daga nashi Bangare Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya wanda kasarsa ke huldar arziki da Sudan a karkashin mulkin al-Bashir fata ya yi na ganin kasar ta Sudan ta gaggauta komawa tafarkin Dimukuradiyya. Sai dai kuma kasar Amirka da Faransa da Jamus da Birtaniya da Beljiyam da Poland daga nasu bangare sun kira zuwa taron gaggawa na kwamitin tsaro na MDD domin nazarin halin da ake ciki a kasar ta Sudan.