Najeriya na ci gaba da haka rjiyar bashi
March 5, 2024Tun daga kama mulkin gwamnatin dai, sababbin 'yan mulkin Tarayyar Najeriyar ba su boye hawa kan turbar bashi a cikin neman mafitar rikicin tattalin arzikin da kasar ke ciki ba. Abujar dai ta karya kumallo da wata aniyarta ta karbar dalar Amurka miliyan 1000 da miliyan 500 cikin watan Nuwambar bara, a cikin sunan bashin daga Bankin Duniya. Kafin kuma a cikin wannan makon gwamnatin Najeriyar ta sake wani sabon shirin na karbar wani bashin dalar Amurka miliyan 2000 da miliyan 700 daga Bankin Raya Kasashe na Afirka, domin noma da ma batun kasafin kudin kasar na shekarar bana. Duk da cewar dai har ya zuwa yanzu ana zangon farko na shekarar, tuni masu mulkin suka kai rabin dalar Amurka miliyan 8000 da gwamnatin ta tsara ci a bana da sunan bashin.
Karin Bayani: Bashi na barazana ga ayyukan raya kasa a Najeriya
Ya zuwa yanzu dai Najeriyar tana biyan Naira tiriliyan kusan tara, adadin da ya kai kaso kusan 80 cikin 100 na kudin shigarta wajen biyan uwar kudi da ma ruwa na basukan da ta diba baya. Kafin dorawa a sabon bashin da ke iya mai da daukacin kudin shigar kasar kafa ta biyan basussuka, maimakon ayyukan raya kasar da ke zaman na kan gaba a zuciyar al'umma. Abun kuma da ya dauki hankalin babban bankin kasar CBN da a wannan mako ya ce kasar tana cikin barazana mai girma, sakamakon karuwar yawan bashin. Gwamnan bankin Oluyemi Cardoso dai ya ce yanda kasar da ma kasashe da yawa ke tafi da harkokin bashin na waje dai, na iya shafar kokarin daidaiton lamura cikin batu na tattalin arzikin da ke tangal-tangal.
Yusha'u Aliyu dai na zaman kwararre ga tattalin arzikin, kuma a fadarsa kasar ba ta bukatar karin bashi yanzu. Bashi cikin batun ginin kasa ko kuma bashingina kai dai, mai da kai zuwa harkar bashin na kara fito da alamun gazawar 'yan mulkin da ke ikirarin sanin makamar mulki cikin batun na tattalin arzikin a fili. Cikin imanin mai da daukacin kasar irin birnin Ikko ne dai, miliyoyin 'yan kasar suka hango haske suka kuma kai ga tabbatar da mulkin Bola Ahmed Tinubu. Legas din a karkashin ikon Tinubu na zaman ta farkon fari da ta yi amfani da haraji wajen sauya rayuwar mazauna birnin, shekaru 20 da doriya can baya.
Karin Bayani: Soke izinin canji: neman gyara ko kassara sana'a?
Makamin yakin neman zabe ga shugaban kuma alkawarin da 'yan kasar ke fatan su gani yanzu, a fadar Ibrahjim Shehu da ke zaman sakataren kungiyar Raya Tattalin Arzikin Arewacin Najeriyar. Ya zuwa karshen watan da ya shude dai basussukan da ke kan jihohi da ma kanta tarayyar sun kai tiriliyan 140, adadi mafi yawa a tarihin kasar da ta kalli afuwar bashin kasa da shekaru 20 da suka shude. Abun kuma da ke dada nuna alamun inda baki yake shiri ya karkata ga gwamnatin da ta hau mulki bisakan alkawarin harajin, amma kuma ke neman harde kafa da komawa zuwa ga basuka da nufin cika alkawarin da ke tsakanin 'yan mulki da 'yan kasa.