Barazanar yajin aikin ma'aikatan Najeriya
July 4, 2024Tuni dai daukacin jami'o'in kasar suka dau harami, a cikin wani sabon rikicin da ke barazana na tsayar da ayyuka a daukaci na jami'o'in kasar. Kungiyoyin manya da kananan ma'aikatan dai, ne da zummar tilasta masu mulkin kasar biyan wani bashin da ya kai na watanni guda cikin albashi da alawus. Tun a watan Maris din wannan shekarar ma'aikatan suka fara gargadi ga Abujar kan ko dai ta daidaita tsakanin malaman da ke koyarwa da ragowar ma'aikatan da ke mata aiki a jami'o'i na kasar, ko kuma masu tallafawa malaman su koma kallo a cikin harkokin jami'o'in. Mohammed Haruna dai na zaman shugaban kungiyar Manyan Ma'aikatan Jami'o'in Kasar SANUU, kuma ya ce da akwai alamun zalunci a kokarin bambanta tsakanin bangarorin da ke jami'o'in a yanzu haka. Kokarin kyautatawa kalilan ko kuma neman rikici a jami'o'in Tarayyar Najeriyar dai ko bayan ma'aikatan su kansu malamai da ragowar ke wa kirari irin na mowa ta gida, sun fara nunin yatsa ga gwamnatin a kan batun albashin.
Kungiyar Malaman Jami'o'in Kasar ASUU dai, na neman sake nazari a kan albashin malamai da ta ce ya tsufa kuma bai zo daidai da abun da ake gani cikin kasar a halin yanzu ba. Dalar Amurka dai na Naira 120 a lokacin da malaman suka nemi karin karshe kafin tashinta zuwa 1,500 a halin yanzu, a fadar Farfesa Abdulkadir Mohammed da ke zaman jagoran jami'o'in da ke a jihohin Kano da Jigawa. Sabon yunkurin mai gaba daya a jami'o'in kasar dai, daga dukkan alamu na shirin yamutsa lamura cikin kasar da masu mulkin ke kokawa cikin neman karin albashin ma'aikatan. Imam Mohammed dai na zaman mataimakin shugaban kungiyar Daliban Najeriyar NANS, kuma ya ce yunkurin ma'aikatan jami'o'in na shafar ayyukan karatun daliban. Tuni dai da ma Abujar tai nisa zuwa batun bai wa daliban damar cin bashi ga dalibai cikin neman hanyar samar da kudin tafi da jami'o'in, a kasar da ke neman hanyar yasar kwallon mangoro cikin batun na karatu.