Najeriya: Yunkurin yaki da cin hanci tare da ICPC
August 2, 2017Duk da cewar hukumar EFCC ta yi kaurin suna tare da buwaya a tsakanin sarakuna dama talakawa na kasar, ga 'yar uwarta ta ICPC dai karatun na kusan kama da karatun kurma ga batun yaki da cin hancin na Tarrayar Najeriya da yanzu haka yake kwan gaba kwan baya. Abun kuma da ya kai gwamnatin kasar sauke shugaba na hukumar ICPC Ekpo Nta, tare da maye gurinsa da Farfesa Bolaji Awosanaye da ake saran zai sake farfado da hukumar tare da kara mata karfi.
A baya hukumar ICPC ba ta yi armashi ba
Tun kafin ga nadin dai dama farfesan na zaman sakatare na majalisar bada shawara ta gwamnatin kan yaki da hanci, kuma daya a cikin manyan jagororin fafutikar. Babban laifin ICPC a karkashin Ekpo Nta dai a fadar ministan shari'a kuma babban jaforan yakin hanci na kasar Abubakar Malami, shi ne na gaza hukunta ko kuda a hukumar da hankalinta ke a kan ma'aikatan gwamnatin kasar a halin yanzu.
Abun da ake jira ga sabon shugaban ICPC
A cikin kokari na gyaran fuska da nufin biyan bukata dai, gwamnatin Tarrayar Najeriya na fatan ganin wannan sabon sauyin zai taimaka wajen kara fadada yaki da cin hancin da ya zuwa yanzu yafi karkata ga masu siyasa da sauran masu rike da manyan mukamai na gwamnati. Ana dai kallon kokari na karfafa ICPC ka iya kaiwa ga kara fadin yakin da nufin tunkarar matsakaita da kanana na ma'aikatan kasar da ake zargi da sata amma kuma suke tsira da abun da suka sata sakamakon gaza cika aikin na hukumar ta ICPC.