1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar- shirin yaki da Boko Haram

Larwana Malam HamiFebruary 9, 2015

Al'umma na nuna goyon bayansu dangane da muhawarar da majalisar dokokin Jamhuriyar Nijar ke yi kan amincewa da tura sojoji zuwa Najeriya domin yakar Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1EYPM
Hoto: DW/M. Kanta

Sojojin hadin gwiwar da za a tura a Tarayyar ta Najeriyar dai na karkashin kawancen rundunar kasashen da ke makwabtaka da Tafkin Chadi wadandada kungiyar ta Boko Haram ke son mamayewa da hare-haren ta'addanci. Kungiyoyin fararen hula da 'yan siyasa da ma masana kan al'amuran tsaro sun fara bayyana ra'ayoyin su tare da bada kwarin gwiwa ga sojojin kasar.

Rundunar Sojojin Chadi a Najeriya
Rundunar Sojojin Chadi a NajeriyaHoto: AFP/Getty Images/M. Medina

Hadin kan bazata

Duk da irin rashin fahimtar juna gami da rarrabuwar kan da al'ummar Jamhuriyar Nijar din ke fuskanta sakamakon rigingimun siyasa, kila wa kalan shigar dakarun kasar cikin rundunar yaki da kungiyar Boko Haram ya kama hanyar sanya 'yan kasar zamowa tsintsiya madaurinki guda. A cewar Habibu Isufu na jam'iyyar adawa ta MNSD Nasara, an ma makara da shiga yakin. Haka su ma dai 'yan mazan jiya wato tsofaffin sojoji masu ritaya ta bakin kwamanda Maman Danbuzuwa sun ce daman sun san za a rina ganin cewa kungiyar ta Boko Haramna ci gaba da fadada hare-harenta.

Nasarorin rundunar taron dangi

Shi kuwa Alhaji Umaru Isa shugaban kungiyar dattawa ta kasa a bari ya huce shi ke kawo rabon wani. A cewarsa tarihi ya nuna irin yake-yaken da kasashen Afrika suka tsinci kansu a baya, kuma rundunar taron dangi ta yi tasiri inda ya ce bai ga dalilan da zai sa a samu tsaiko ba a wannan karon ma. A yanzu haka dai hankulan jama'ar kasar sun karkata ga batun shigar sojojin kasar cikin yaki da kungiyar ta Boko Haram da ya kama hanyar zama farilla ga gwamnatin ta Nijar duba da yadda aka fara samun harin 'yan kunar bakin wake a yankin kudu maso gabashin kasar musanman ma a Jahar Diffa.

Masu gwagwarmaya da makamai a Najeriya
Masu gwagwarmaya da makamai a NajeriyaHoto: picture alliance/AP Photo