1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Lafiya

Kalubalen aikin ungozoma a Afirka

May 4, 2022

Ungozoma da suke kula da mata masu juna biyu da kuma karbar haihuwa a kasar Kenya, na kokawa kan yadda ayyuka ke musu yawa.

https://p.dw.com/p/4Apil
Ghana |  Mata ma su Juna Biyu
Aikin ungozoma na fuskantar kalubale a kasashe da dama na AfirkaHoto: DW/M. Suuk

Aikin ungozoma na da matukar mahimmancin a rayuwar al'umma mussaman ga mata, ta la'akari da yadda suke kula da mata masu juna biyu yayin lalurorin ciki da haihuwa da kuma lokacin jego. Da dama na ganin a yanzu ana samun karin wadanda ke nazari a fannin ungozoma a manyan makarantun kasar Kenya, inda a yanzu aka aje tsarin aikin a gargajiyance. Rahotannin sun tabbatar da cewa kimanin kaso 70 cikin 100 na ungozoma a Kenya, na kokawa kan irin tarin aikin da ke gabansu. A dangane da haka ne wata kungiya mai zaman kanta a kasar ta "What Women Want", ta ce akwai bukatar a samarwa mata da kuma jarirai dukkan wani taimako na gaggawa idan bukatar hakan ta taso. A ra'ayi irin na Anne Nguku da ke zama shugabar kungiyar kuma ungozoma, lokaci ya yi da za a magance dukkan wasu kalubale da ungozoma ke fuskanta a ayyukansu.