Zabiya da tsangwama a Tanzaniya
October 14, 2015Wasu dai sun aminta da cewa amfani da sassan jikin nasu na iya kaiwa ga cimma buri da aka sa a gaba, haka kuma 'yan tsubbu kan biya mukudan kudade don mallakar Zabiyan don yin ayyukan juju da su.
Sai dai duk da wannan kyama da suke fuskanta, wani Zabiya ya zama dan jarida wanda kuma yake fafutukar kawo sauyi akan wannan al'amari.
Henry Mdimu ya kasance dan jarida wanda ya sha alwashin wayar da kan al'umma kan irin tsanar da aka yi musu ta hanyar aikinsa.
"In dai zaka dauki rayuwarka da zafi, to babu in da mutum zai je, dan haka ina alfahari tare da cigaba da gudanar da al'amura".
Shi dai Henry sau biyu yana tsallake rijiya da baya a hare-haren da ake kai masa na sace shi, amma kuma hakan bai karya masa gwiwar ci-gaba da gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum ba, wanda hakan shi ne abin da ya ja hankalin matarsa Angel wadda ita ma 'yar jarida ce da kuma suke gudanar da rayuwarsu cikin annashuwa, su na da 'ya'ya uku wadanda kuma suke alfahari da su kamar yadda ta yi karin haske.
" A lokacin da muka fara soyayya, sai mutane suka fara cewa ina son sa ne saboda yana da abin duniya, yanzu kuma da suka ga mun samu 'ya'ya uku sai suka ce yayi mini asiri, abubuwa da dama sun wakana, amma bana san na fiya yawan magana".
Mutane da dama a kasashen Gabashin Afrika musamman Tanzaniya na yi wa Zabiya kallon dodanni, wanda canja hakan ke zama wani babban kalubale, dalilin da ya sanya Henry mayar da hankali wajan yin shirye-shiryen dora mutane kan hanya dangane da karyata hakan.
Henry ya dauke ni zuwa ofishin "Same Sun" wata kungiya da ke kare hakkin Zabiya, kuma tana samar da tallafin gaggawa da kuma bayar da mafaka ga Zabiyan. Mariam Stanford an yanke mata damatsanta a lokacin da aka kai mata wani hari don mallakar wani bangare na jikinta kamar yadda ta ke karin bayani.
"Wani lokacin na kan yi mafarki an yanke min hannu, amma duk da hakan na godewa Allah ganin yadda na rage irin wadannan muggan mafarke mafarke".
Acewar Vicky Ntetema darakta a kungiyar Same sun suna iya bakin kokarinsu wajan bibiyar irin cin zarafin da aka yi wa masu lalurar,
Su dai Zabiya na fuskantar cin zarafi a koda yaushe, a yayin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama ke cigaba da kiraye-kirayen cewa ya kamata gwamnati ta kara zage damtse wajan hukunta masu wannnan mummunar dabi'a. Wannan dalilin ne ya sanya Henry Mdimu ya lashi takobin ganin ba zai yi kasa a gwiwa ba wajan ci-gaban fafutukar kwato hakkin zabiya ta yin amfani da basirar da Allah ya huwace masa.