Alassane Ouattara bai bayyana matsayinsa ba
July 21, 2020Mutuwar firaminista Amadou Gon Coulibaly ta dagula duk wani lisafin da jam'iyyar RHDP mai mulkin Cote d'Ivoire ta yi game da zaben watan Oktoban da ke tafe, inda a yanzu ya zama tilas jam'iyyar ta nemi wani sabon dan takara da ke iya samun amincewar daukacin 'yan jam'iyyar, mutumIn da kuma ka iya dorawa daga inda shugaban Alassane Ouattara ya dakata.
Magoya bayan Alassane Ouattara na yin kira da ya tsaya takara a zaben watan Oktoba
Da dama ne daga cikin magoya bayan jam'iyyar da ke yin mulki ke yin kira ga Alassane Ouattara da ya tsaya takara duba da matsayinsa da kuma kimarsa a idanun duniya. Malam Touré Mamadou ministan matasa ne da samar da aikin yi kuma kakakin jam'iyyar RDPH mai mulkin kasar: "'Yan jam'iyyarmu da dama na tsokaci domin ganin shugaba Ouattara ya ci gaba da kasancewa a kan madafan iko ta hanyar tsayawa takara, daga farko ya amince da cewar ba zai sake tsayawa, to amma kuma yanzu duba da halin da muke ciki na wani yanayi, ya rage ga shugaban ya fitar da wani hukuncin da yake ganin zai dace da yanayin da muka tsinci kanmu."
Alasssane Ouattara bai bayana ba ko zai tsaya takara ba har yanzu
Ga masu yin sharhi a kan harkokin yau da kullum irinsu Geoffroy Kouao akwai alamun cewar Ouattara zai yi takara: " A kasa ga watanni kafin zaben shugaban kasa jam'iyyar da ke mulki ta fada cikin wani yanayi na rashin wani wanda zai iya tunkarar dan takarar hamayya kuma tsohon shugaban kasa Henri Konan Bédié da ba shakka ka iya samun goyon bayan Laurent Gbagbo da jam'iyyar FPI, don haka jam'iyyar Ouattara na cikin wani halin da shugaban ne kadai ka iya tsayawa takara kuma ya lashe zaben. Har yanzu dai shugaba Alassane Ouattara bai bayyana matsayinsa na ko ya amince da kiran magoya bayan jam'iyyarsa ko akasin haka ba game da batun tsayawarsa takara.