Rikicin kabilanci ya ki cinyewa a Sudan
October 21, 2022Bayan halaka mutane da dama da aka yi a dukan bangarori da ke rikici da juna, an kuma kone daruruwan gidaje, lamarin da ya tilasta wa mutane kimanin dubu 65 tserewa su bar mahallinsu. Wata Bahaushiyar Sudan mai suna Khadija Umar Babaji ta ce: " Gwamnati ce ke taimaka musu ko take daure musu gindi. Idan ba haka ba, ta ya ya ('yan kabilar Berta) za su karkashe 'ya'ya da mazajenmu. sun kwashe mana kaya kuma sun wanye lafiya, ni kaina ban san inda mijina ya shiga ba."
Wannan rikici na neman zama ruwan dare
Wannan dai shi ne karo na biyu cikin tsukin watanni uku da kabilun na Hausawa da Berta ke gwabza fada gami da kona wa juna gidaje da gonakai, duk kuwa da jibge Karin jami'an tsaro a yankunansu da ke jahar Nile Blue ko Annilul Azraq a Larabce da hukuma ta yi. Abubakar Yunus daya daga cikin dattawan Hausawa a yankin ya danganta rashin kawo karshen rikicin da rashin aiwatar da doka yadda ya kamata:
Ya ce: "Kowa ya sani a tarihin Sudan, ba a taba samun rikici da Hausawa ba, sai a 'yan shekarun nan, bayan da mahukunta suka yi sako-sako wajen aiwatar da doka. Wannan ne ke ba wa wasu karfin halin kokarin kwace wa Hausawa dukiya da kadarorinsu tare da kokarin korarsu daga kasar baki daya. An sake duk wadanda aka kama a rikicin. A gaskiya ina son samun zaman lafiya. Dole ne a yi bincike ba da wata rufa-rufa ba, a kuma hukunta masu laifi."
Dangantakar rikicin da siyasa
Abdulfattah Altakruri, wani malamin jami'a a Sudan ya ce barkewar rikicin kabilanci na baya-bayan nan ba ya rasa nasaba da dambaruwar siyasa: Ya ce: " Irin rikicin da aka yi a yankin Darfur ne ya zo mana wannan yankin namu na Hausawa, musamman a yanzu da aka ga 'yan takara Hausawa na da farin jinni lashe zabuka, don haka ake son tarwatsa magoya bayansu don raba su da mulkin yankin."
A nasu bangaren, 'yan Kabilun Berta da ke daukar Hausawa baki a yankin suka ce ba zu yarda da kokarin kaka-gidan da Hausawa ke yi a yankunansu ba. Barkat Najjar, daya ne daga cikin yan siyasar Kabilar ta Berta ya ce: "Hausawa sun yi kokarin kafa masarauta da za su hadiye sauran kabilun da ke yankin karkashin sarautarsu, shi ya sa mutane ke tayar da kayar baya domun su baki ne a yankin, ba asalin yan kasa ba ne."
Masana na ci gaba da bayyana wa mutane cewa babu wanda ke yin nasara a duk lokacin da ake kashe-kashen kabilanci.