Sabon fada ya barke a Sudan ta Kudu
August 15, 2016Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ne ya amince da tura dakarun kiyaye zaman lafiya duk da adawar da mahukunta a Juba suka nuna. Rundunar wadda za'a jibge a Juba babban birnin Sudan ta Kudu an ba ta umarnin amfani da dukkan matakan da suka zama wajibi domin kawo karshen tarzoma.
Majiyoyi a rundunar sojin Sudan ta Kudu sun tabbatar a ranar Lahadi cewa fada ya sake barkewa a Juba babban birnin kasar tsakanin sojoji masu biyayya ga shugaban kasar Salva Kiir da kuma sojoji da ke goyon bayan abokin hamaiyarsa, mataimakin shugaban kasa Riek Machar.
Fadan ya barke ne kusa da wani barikin soji da ke daura da gidan shugaban kasar a Juba. Archbishop Paulino Lokudu wanda shi ma ya ce ya jiwo karar harbe harben bindigogi da na makaman atilare, ya bukaci bangarorin biyu su tsagaita wuta.
"Mun damu da yanayin tabarbarewar tsaro a wannan lokaci. Ana kashe-kashe da kwasar ganima. Wajibi ne sojoji su kawo karshen wannan lamari. Muna rokon sojoji su nuna sanin ya kamata da martaba 'yan uwansu maza da mata."
A lokacin da fada ya barke a watan Disamba shekarar 2013, shugaba Salva Kiir daga kabilar Dimka masu rinjaye ya zargi tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Mashar dan kabilar Nuer da shirya masa makarkashiya domin hambarar da gwamnatinsa.
An kashe dubban jama'a galibinsu fararen hula yayin da wasu miliyoyi kuma suka tagaiyara. A bara yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar raya cigaban tattalin arzikin kasashen Gabashin Afirka IGAD ta shiga tsakani ta haifar da kafa gwamnatin hadakar da ake da ita a yanzu.
To amma fada ya sake barkewa a farkon watan Yuli yayin da kasar ke bukukuwan cikar ta shekaru biyar da samun yancin kai daga Sudan.
A ranar Juma'a kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya amince ya tura runduna mai karfi ta sojin yankin su dubu hudu domin shawo kan tarzoma da rashin kwanciyar hankali da suka dabaibaiye kasar a tsawon shekaru uku da suka wuce.
Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya dai ya yi barazanar kakabawa Sudan ta Kudu takunkumin hana sayar mata da makamai idan har gwamnatin ta ki bada hadin kai ko kuma ta haifar da cikas ga ayyukan rundunar tsaron ta soji.