1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakamakon wucin gadi na zaben Laberiya

Ramatu Garba Baba
October 13, 2017

Yayin da ake jiran cikakken sakamakon karshe na zaben shugaban kasar Liberiya, sakamakon wucin gadi na nuni da cewa tsohon shahararren dan wasan kwallon kafa George Weah yana kan gaba.

https://p.dw.com/p/2lmXq
Libera, George Weah
Hoto: Getty Images

Hukumar Zaben kasar Laberiya Jerome Korkoya ya bayyana sakamakon wucin gadi na zaben zagayen farko da ya dauki hankali a ciki da wajen kasar, mutanen kasar dai sun fito kwansu da kwarkwatansu domin ganin sun zabi shugaban da zai kawo sauyin da kasar ke bukata, 'Yan takara 20 ne suka fafata a wannan zabe domin maye gurbin Shugaba Ellen Johnson Sirleaf mai barin gado.

Hukumar zaben kasar ta yi saurin fidda sanarwa bayan fadin sakamakon farkon inda ta bukaci ‘yan kasar da su kawar da kai game da duk wani sakamako na daban muddun ba daga hukumar zaben ba ya fito. Jerome Korkoya shugaban hukumar zaben Liberiya ya tabbatar da haka.

Yanzu dai ana bukatar dan takara ya lashe fiye da kashi hamsin cikin dari daya na kuri'un da aka kada in kuwa aka gagari samun wannan sakamakon to za a je zagaye na biyu, abin lura a nan dai shi ne ga alamu za a wanye lafiya ganin yadda yanzu aka yi nasara na gudanar da wannan zaben cikin lumana.