1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Saudiyya ta fara sauya manufofinta a Afirka

Mouhamadou Awal Balarabe
November 8, 2017

Matakin Saudiyya na canja manufofin arziki da zamantakewa ya fara tasiri a kasashen Afirka. Ko da shi ke a baya ta saba zuba magudan kudi wajen raya mazhabar sunna a Afirka, amma a yanzu tafi raja'a kan tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/2nBZf
Senegal Touba Große Moschee Sufi Bruderschaft
Hoto: picture-alliance/AA/A. Gueye

Daular Saudiyya ta yi amfani da dimbin arzikin da Allah ya hore mata wajen samar da kayayykin more rayuwa a Afirka, inda ta gina masallatai da makarantun isalamiyya da asibitoci a kasashe matalauta na nahiyar. Sannan ta samar da guraben karo ilimin tauhidi a jami'o'inta tare da aika masu wa'azi kasashen Afirka da ke da Musulmi. Saboda haka ne ake zargin masarautar da amfani da kudadenta wajen yada Wahabiyanci a nahiyar ta Afrika.Su ma Kungiyoyi da ke fafutuka da makamai irin su Al-Shabaab, AQMI ko Boko Haram suna koyi ne da wannan akida.

Mouhamed Ndiaye, jagoran 'yan Sufi a Dakar babban birnin Senegal ya ce yana kawo sabani tsakanin mazhabobin biyu. Ya ce" Suna kokarin karkatar da hankalin matasa daga Darika. Muna ganin kamar su na koya wa yara saba wa iyayensu. Sai dai abin takaici su na samun nasara wajen durmiyar da wasu matasa masu zaman kashe wando saboda akwai dan abin sayan na goro da ke basu."

Saudi Arabien Kronprinz Mohammed bin Salman
Yerima mai jiran gado na Saudiyya ne ke aiwatar da sauye-sauyeHoto: Getty Images/AFP/F. Nureldine

Baya ma ga addini, Saudiyya ta sauya wasu daga cikin manufofinta a Afirka, inda a yanzu ta fara zuba jari a ayyukan gona a nahiyar. Mujallar Financial Times ta nunar da cewa kasa mai tsarki ta zuba kusan dala miliyan dubu hudu a Afirka a shekara ta 2016. Jens Heibach, kwarwarre ne a al'amuran da suka shafi Saudiyya a cibiyar GIGA da ke Hamburg a Jamus ya ce karancin kudin shiga ne ya sa masarautar Saudiyya sauya alkiblarta ta tattalin arziki.

"An kara gano Afirka a matsayin nahiya ta zuba jari da huldar kasuwanci wacce Saudiyya za ta iya amfana. Kasancewa tana kokarin sake fasalin tattalin arziki da siyasarta, ya sa Afirka ke da muhimmanci a gareta, ba wai don kara wa sarki kima ba kawai, amma don Janyo hankalin masu zuba jari na kasashen waje."

Sai dai Yerima Mohammed Salman mai jiran gado na Saudiyya, na da jan aiki a gabansa wajen aiwatar da sauye-sauye kasancewa akasarin 'yan gidan sarautar da ke tafiyar da harkokin mulki masu ra'ayin rikau ne.