Sabon tsaftace Ka’aba da Harami
April 21, 2021Mahukuntan Saudiyya sun gabatar da sabbin dabarun tsaftace Ka'aba da farfajiyar Harami cikin karamin lokaci da kuma busar da shi, ba tare da an samu dogon tsaiko ga masu ibada ba, kamar yadda kamfanin dillancin labaran kasar Saudiyya ya bayar da rahoto.
A karon farko a tarihi an gudanar da aikin wanke dakin Ka'aba da farfajiyar masallacin harami mai tsarki a cikin lokaci mafi karanci, inda ma'aikatan da suke kula da tsaftar wurare masu tsarki su kimanin dubu hudu suka gudanar da aikin a cikin kasa da mintuna biyar suka kuma kammala.
A cewar mahukuntan ad suke da haramomi masu tsarki na Makka da Madina, wannan shi ne karon farko da aka taba yin irin wannan aiki a cikin kankanin lokaci a tarihi. Yareer Abdul Sammad shi ne jami'in kula da harkokin tsaftace Haramin na Makka da Madina:
"Da ikon Allah, albarkacin sabbin na'urorin tsafta na zamani da ke aiki cikin sauki da gaggawa, mun samu damar tsaftace Harami cikin 'yan dakiko, ba tare da an yi ta kwashe mutane ana kai su wata kusurwar ba. Wannan babban abin farin ciki ne da zai saukakawa maniyyata ayyukan ibadarsu ba tare da kawo musu tseko ba."
Fadin wajen da ake wankewa a kullum ya kai murabba'in mita dubu 700. Sannan idan an kammala aikin fadada masallacin, girman wajen da ake wankewa zai kai murabba'in mita miliyan daya da dubu dari takwas.
Mutum dubu 27 ne ke aikin wanke wuraren na ibada, yayin da mutum 100 ke sa ido wajen ganin an yi tsaftace wuraren yadda ya kamata. Akwai kuma motoci 40, da motocin daukar shara 120, da motoci 60 na musamman masu wanke wuraren ibadar da ake amfani da su yau da gobe. Kimanin mutane 291 ne suke tattara sharar da aka tara tare da zubar da ita ba tare da bata lokaci ba.