Shugabannin ECOWAS za su gana a Abuja
December 15, 2024Ficewar kasashen uku dai ka iya kara dagula al'amurra musamman ma ta fannin tattalin arziki da shige da fice da tsaro da ke addabar yankin na yammacin Afirka.
Ministocin harkokin wajen kasashen uku na AES sun kara jaddada matsayarsu ta ficewa daga kungiyar, tare da shata makomar shige da fice da za ta kasance a tsakanin 'yan kasashen Ecowas da kasashen uku.
Shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye da kungiyar ta dora wa alhakin shiga tsakani, zai gabatar da nasa bahasi, tare da samar da wata sabuwar taswirar da ka iya kawo masalaha.
Ko baya ga batun kasashen Mali da Burkia Faso da Nijar da ke zama a kan ajandar taron, shugabannin na Ecowas /Cedeao za su kuma tattauna batutuwan da suka shafi tsaron yankin, da ma batun shirya zabe a kasar Guinea Conakry.
Karin Bayani: ECOWAS ta ji zafin rashin mambobinta uku