al-Burhan zai ci gaba da jagorantar Sudan
November 12, 2021Jerin sunayen membobin sabuwar majalisar rikon kwaryar Sudan ya kunshi sojoji biyar da farar hula shida, gami da jagororin 'yan tawaye masu dauke da makamai uku da aka yi sulhu da su. Wannan mataki na nuni da cewa har yanzu ba ta canja zani ba, ganin cewar shugaban sojin zai jagoranci majalisar, yayin da Mohammed Hamdan Daglo, shugaban rundunar sojin kai daukin gaggawa zai zama mataimakinsa.
Wannan na zuwa ne makonni biyu bayan da al-Burhan ya rusa gwamnatin Firaminista Abdallah Hamdok wanda ake ci gaba da yi wa daurin talala, gami da ayyana dokar-ta-baci a fadin kasar ta Sudan. Kazalika garambawul din na zuwa ne kwanaki biyu gabanin wata gagarumar zanga-zanga da masu fafutukar neman sauyi suka kira, domin ganin bayan juyin mulkin ranar 25 ga watan Oktoban 2021.
Ra'ayoyi sun bambanta kan gwamnatin rikon kwarya a Sudan
Tuni aka fara martini kan wannan sabon matakin da ke zuwa bayan lalacewar 'yunkurin dawo da gwamnatin Abdallah Hamdok, wanda ya dage kan cewa ba zai taba yarda ya zama shugaban jeka na yika ba. Wasu 'yan Sudan sun yi ammanar cewa duk da rajin kafa dimukaradiyya a kasar, nesanta sojoji da wasu madafun ikon na iya zama barazana ba ga tafarkin dimukaradiyya kadai ba, har ma da tsaron kasar:
Wasu da ke yaba wa matakin sun ce zai kawo karshen zaman kara zube da aka shiga a kasar tun bayan juyin mulkin sojin. A nata bangaren, gamayyar 'yan kwadagon kasar ta Sudan da a baya ta nemi a shiga yajin aikin gama gari da kuma gudanar da zanga zanga mafi dandazo don tirsasa wa sojojin lashe amansu da dawo da halin da ake a kasar kafin juyin mulkin, ta ce matakin kafa sabuwar gwamnatin,,wata yaudara ce ta gyara wa mulkin soji gindin zama a kasar.
Majalisar Dinkin Duniya na neman bakin zaren warware rikicin Sudan
Duk wannan na gudana ne a daidai lokacin da kwamatin sulhu na MDD ke shirin gudanar da zama na musamman kan makomar kasar ta Sudan. Mona Yuly, wakiliyar kasar Norway da za ta jagoranci zaman taron, ta ce har yanzu akwai bukatar sojojin na Sudan su gyara kura-kuransu, inda ta ce: "Mu nyi ammanar cewa har yanzu ba'a makara ba. Dage daurin talala ga Hamdok, da ba shi damar gudanar da ayyukansa ba tsangwama ,shi ne matakin da zai iya gamsar da al'ummar Sudan da ma sauran kasashen duniya."