Sudan: Fafutukar neman samun canjin mulki
January 31, 2019Talla
Zanga-zangar dai ta samo asali ne sakamakon karin kudin biredi tun a watan da ya gabata kafin daga baya ta juye ta zama ta neman shugaban kasar Omar al Bashir da ya sauka daga mukaminsa. Yanzu haka dai mako na takwas ke'nan da al'ummar kasar daga garuruwa daban-daban ke neman sauyin gwamnati a Sudan, a bangaren kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun baiyana cewar adadin mutanen da suka rasa ransu ya kai 100 yayin da gwamnati ta baiyana mutane 29 da suka mutu. Jam'iyyun siyasa sun raba gari da gwamnati, jam'iyya ta baya-bayan da ta sanar da yin hannu riga da gwamnatin kasar ta sudan itace jam'iyyar Umma.