Sudan: Dambarwar rikicin juyin mulki
October 28, 2021Talla
Juyin mulkin na Sudan ya janyo martani na kasashen duniya wadanda suka bukaci sojojin su mayar da kasar tafarki.
Kwamintin sulhun Majalisar Dinkin Duniya da shugaban Amirka Joe Biden sun yi kira a gaggauta mayar da gwamnatin farar hula da sojojin suka hambarar.
Duka mambobin kwamitin sulhun sun baiyana matukar damuwa da juyin mulkin wanda ya mayar da kasar baya.
Janar Abdel-Fattah al-Burhan wanda ya jagoranci juyin mulkin da ya hambarar da tsohon shugaba Omar al-Bashir bayan zanga zangar gama gari ta matasa ya rusa gwamnatin kasar da ke tangal tangal.