Adawa da juyin mulkin soji a Sudan
October 25, 2021Biyo bayan ayyana juyin mulki da sojojin Sudan suka yi wa gwamnatin rikon kwaryar kasar da Firaiminista Abdallah Hamdok ke jagoranta, 'yan kasar na ci gaba da mayar da martanoni mabanbanta.
Kusan a iya cewa birnin Khartoum da ke zama fadar mulkin kasar ta Sudan ta yi cikar kwari da dubbun dubatan masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin wannan Litinin, duk kuwa da sanya dokar ta baci da sojojin suka yi, gami da yunkurin fasa masu zanga zanga da karfin tuwo da sojojin suka yi, yadda tashar Aljazeera ta sanar da jikkata masu zanga-zanga da dama.
Kungiyar Ahuriyyah wal Adaah, wato ''Yanci da Adalci'' ta matasan da suka jagoranci zanga-zangar da ta kai ga kifar da gwamnatin Oumar al-Bashir shekaru biyun da suka gabata, ita ce ta nemi daukacin 'yan kasar da su fito don kalubalantar juyin mulkin da jagora a Kungiyar Mamdouh Abdulgani ya siffanta shi da kokarin yin kisan mummuke ga tarin burin al'ummar Sudan na samun sauyi da 'yanci. "Ba za mu lamunta da mulkin sojoji ko na kama karya ba, bayan sadaukar da kan da muka yi mu kai juyin juya hali. Dola ne a dawo da gwamnatin Hamdok a kuma hukunta wadanda suka kitsa yi wa 'yan Sudan fashin 'yancinsu."
Tuni gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar, wacce ita ma ta taka gagarumar rawa wajen zanga-zangar kifar da gwamnatin Oumar al-Bashir, ta nemi ma'aikatan kasar da su shiga yajin aikin sai baba ta gani, yadda kungiyar ikitoci da malaman jami'a da direbobin kasar suka sanar da amsa wannan kiran.
Da safiyar wannan Litinin, aka wayi gari da kwaramniyar sojoji a kan manyan titunan birnin Khartoum, yadda daga baya shugaban rundunar sojin kasar Abdulfattah Burhan ya fito ta kafar watsa labaran ya sanar da sanya dokar ta baci da rusa gwamnatin rikon kwaryar da Abdallah Hamdok ke jagoranta, bayan da aka kwashe kwanaki ana zanga-zangar adawa da gazawarta, wasu ma ke kira ga sojoji da su kifar da ita.
Duk da cewa yayi alkawarin ci gaba da aiwatar da shirin mika mulki ga farar hula a wa'adin da aka yanke karshen watan Yulin shekarar 2023 da kuma mutunta yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a birnin Juba da kungiyoyi masu tayar da kayar baya da ke daukar makamai a kasar, gami da kafa sabuwar gwamnatin rikon kwaryar ta kwararru da za ta wakilci dukkanin bangarorin kasar, amma masharhanta na dama na tababa kan hakan.