1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan ta Kudu: Ci gaban nuna yatsa tsakanin masu adawa

Zainab Muhammed AbubakarNovember 13, 2014

Tuni dai Kungiyar IGAD ta kasashen da ke gabashin Afrika ta yi barazanar amfani da karfin soji wajen kawo karshen rikicin, da ke ci gaba da faruwa tsakanin bangaren gwamnati da 'yan awaren wannan kasa.

https://p.dw.com/p/1DmMC
Ehtiopien Addis Abeba Friedensverhandlungen Südsudan 06.11.2014
Hoto: picture-alliance/Minasse Wondimu/Anadolu Agency

A ranar Asabar da ta gabata ne dai shugaba Salva Kiir na Sudan ta kudu da jagoran adawa Riek Machar suka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Adisababa kasar Ethiopia. Shugaba Kiir ya yi alkawarin cewar dakarun gwamnati za su cigaba da kasancewa a barikinsu, kuma za su yi fada ne kawai idan bukatar kare kansu ta taso, wannan kazalika shi ne alkawarin da Machar ya dauka a madadin mayakansa.

Watannin 11 kenan da wannan jaririyar kasa a Afrika ta tsinci kanta cikin yakin basasa, bayan da shugaba Kiir ya kori tsohon mataimakinsa Riek Machar, wanda ya yi yunkurin kifar da mulkinsa. Rikicin da a yanzu haka yake dangane da kabilanci, tuni ya yi sanadiyyar rayukan mutane dubu 10, baya ga wasu miliyan biyu da suka tsere daga matsugunnensu.Tun a farkon rikicin ne dai kungiyar gamayyar kasashen gabashin yankin watau IGAD ta yi kokarin shiga tsakani, kamar yadda ta taka rawa wajen cimma wannan yarjejeniya da ta ruguje. A cewar Andrews Atta-Asamoah da ke cibiyar nazarin harkokin tsaro a Afrika ta kudu dai akwai bukatar IGAD ta kara matsa kaimi:

Salva Kiir Präsident Südsudan 05.11.2014 Juba
Hoto: Reuters/J. Solomon

"Ina ganin lokaci yayi da kungiyar IGAD zata bar rawar da take takawa na mai shiga tsakani da jagorantar tattaunawa, ta fito fili karara ta bayyana goyon bayanta ga muradun al'ummar Sudan ta Kudu na bukatar kawo karshen wannan rikici".

Shi kuwa tsohon Darektan fannin siyasa na tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Peter Schumann, bayyana shakku ya yi dangane da matsayin kungiyar ta IGAD:

"Kwanan nan na dawo daga Kenya da Juba, kuma na samu damar tattaunawa da masu shiga tsakanin da masu ruwa da tsaki a rikicin, tambayar da kowa ya kasa amsawa ita ce, shin kungiyar tana da karfi ko kuma ikon sanya takunkumi tare da tabbatar da aiwatar da takunkumin?".

Kasashen duniya dai sun bukaci da a warware wannan matsala a siyasance, inda kungiyar yankin gabashin Afirka ta bawa shugaba Kiir da abokin adawarsa Machar kwanaki 15 na tattauna yiwuwar kafa gwamnatin hadin kan kasa. A yanzu haka dai baya ga matakan takunkumin tafiye-tafiye da na rike kaddarori da cinikin makamai, IGAD ta yi barazanar amfani da karfin soji wajen kawo karshen rikicin.