Gaza shawo kan rikicin Kogin Nilu
September 16, 2020Habashan dai ta ce ta dukufa wajen gina katafaren dam din ne da nufin wadata kasarta da wutar lantariki, abin da ya sanya kasashen uku da ke makwabtaka da juna wato Sudan da Masar da ita kanta Habashan, suka samu kansu cikin cece-kuce. Wannan takaddamar da har yanzu aka gaza shawo kanta bayan hawa teburin tattaunawar tsawon lokaci dai, na ci gaba da zama kadangaren bakin tulu ga zamantakewar al'ummomin wadannan kasashe, sabanin a baya da ake alfahari da wannan kogi. Fitaccen mawakin kasar Masar Mohammed Abdelwahab ya taba rera wakar da yake bayyana Nilu a matsayin basarake daga kasar Habasha, wakar da idan ya yi ta a yanzu zai iya tsintar kansa cikin wadi na tsaka mai wuya daga bangaren kasarsa ta Masar. Lamarin dai ya kara muni musamman bayan da gwamnatin Addis a 'yan makonni da suka shige, ta yi kokarin gabatar da hujjojinta.
A babban birnin kasar Addis Ababa, daruruwam mutane sun yi ta rawa da wake wake a kan tituna a farkon watan Augustan da ya gabata, dauke da tutocin kasar mai launin kore da dorawa da ja. Zenash daya ce daga cikinsu: "Mun zo nan ne domin mu bayyana farin cikinmu na ganin cewar an cika dam din ma'ajiyar ruwanmu. Na rasa kalaman da zan yi amfani da su domin bayyana farin cikina. Ina goyon bayan gwamnatinmu, kuma wajibi ne na nuna cewar ina tare da su. Ya zuwa yanzu muna gasa burodinmu ne da gawayi, amma kammala wannan dam na nufin samun wutar lantarki."
Karin Bayani: Habasha ta kauracewa yarjejeniyar Nilu
Wannan dai shi ne alkawarin da gwamnati ta yi wa al'umma, samar musu da wutar lantarki. Kusan kaso 65 daga cikin 00 na al'ummar Habashan ne dai basu da wutar lantarki.
Sai dai labarin zai sauya, da zarar an kammala akin gina dam mafi girma a tarihin Afirka da zai yi ajiyar ruwa da yawansa zai kai megawatt 6,000. Haka kazalika, zai bai wa kasar damar fitar da wutar lantarkin har zuwa kasashen Sudan da Kenya da Djibouti da ke makwabtaka.
Karin Bayani: Fahimtar juna a rikicin Kogin Nilu
Peter Kagwanja masanin kimiyyar siyasa ne a kasar Kenya: "Habasha na bukatar wannan katafaren dam domin cire mafi yawan al'umarta daga matsanancin talauci. Tana bukatar dam din, domin samar wa masana'antu wutar lanatarki, da bai wa makwabtanta damar samun lantarki mai rahusa. Ta haka ne za mu cimma kafa habaka tattalin arzikin yankin."
A cewar nasanin kimiyyar siyasar dai, ba za a taba kwatanta Habashan da Masar wadda tuni ke da albarkatun mai da manyan tashoshin samar da wutar lantarki guda biyu ba, a yayin da a yanzu ne Addis Ababa ke rarrafen fitar da al'ummar daga cikin talauci ta hanyar samar musu da wutar lantarki. Yunkurin sasanta rikicin da ya dabaibaye Kogin Nilun dai ya ci tura. Masar na tsoron yankewar ruwa. Wannan kasa da ke cikin sahara na dogaro ne da kogin, ga shi yanzu ta daina samun tallafin kasa da kasa. Ita ma Amurka rage tallafin da ta ke baiwa Ethiopiya, batu da za a gabatar a tattaunwarsu ta gaba.
Karin Bayani: Shugabannin AU za su tattauna rikicin Nilu
A matsayinta na zama kasa ta uku Sudan na taka-tsan-tsan a wannan takaddama. Sai dai kasar da ke zama makwabiyar Habasha, ita ma na tsoron fuskantar matsalar karancin ruwa. Sai dai a yanzu haka Sudan din na fama da ambaliyar ruwa, abin da Habashan ke cewar, idan har an yi kyakkyawan amfani da dam din, to ko shakka babu kogin na Nilu ba zai yi ambaliya ba.