Sudan: AU ta nemi soja su gaggauta mika mulki
April 16, 2019Duk da nasarar da suka yi na sauke tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir da ya shafe tsawon shekaru 30 kan madafan iko da Janar Bin Auf kasa ga 'yan kwanaki, har yanzu masu zanga-zangar ba su yi sanyi a gwiwa ba ganin yadda suke cewa sojojin na kokarin yi musu sakiyar da baruwa, musamman bayan yunkurin fasa zaman dirshin sai baba ta gani da masu zanga-zangar ke yi wanda sojin suka ce masu boren su yi a ranar Litinin.
A cikin sauti da rera wakoki masu zanga-zangar sun bayyana cewa suna nan sai an biya bukatunsu ko da kuwa za su mutu a dandalin na gwagwarmaya, suna masu nuna fatan ganin an damka gwamnatin farar hula mai cikakken iko wacce su kansu sojojin da suka yi juyin mulkin za su kasance karkashin ikonta har na tsawan shekaru hudu.
Tuni kwamatin sulhu na Kungiyar Tarayyar Afirka ya bai wa sojojin na Sudan wa’adin kwanaki 15 don su mika mulkin ga fararan hula ko su fuskanci mayar da su saniyar ware a cikin jerin kasashen Afirka.
Matakin da sojojin kasar Sudan suka dauka na ceton kasar na amsa kiran masu zanga-zangar ne a cewar wani kusa a hukumar mulkin sojan Sudan yana mai cewar ba da jimawa ba za su sake mika mulki kan tafarkin dimokuradiyya.