1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar bangarorin Sudan ta Kudu

Abdourahamane HassaneOctober 9, 2014

Kasashen duniya na kara matsin lamba ga bangarorin da ke gaba da juna a Sudan ta Kudu kan su sake komawa kan teburin sulhu domin kafa gwamnatin hadin kan kasa.

https://p.dw.com/p/1DSfX
Riek Machar und Salva Kiir
Hoto: Ashraf Shalzy/AFP/Getty Images

Kasashen duniyar dai na fatan sake zama kan teburin sulhu ne kawai zai kawo karshen yakin basasar da aka kwashe sama da shekara guda ana yi tsakanin Shugaba salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar, wanda kuma ya dai daita kasar ta Sudan ta Kudu. Kungiyar kasashen gabashin Afirka wato IGAD ta debawa bangarorin biyu wa'adin zuwa Alhamis din nan tara ga wannan wata na Oktoba da su sulhunta tare kuma da kafa gwamnatin hadin kan kasa ko kuma su fuskanci fushinta.

To amma wa'adin ya cika ba tare da samun wani sauyi ba abunda ya sa kungiyar ta IGAD ta tsawaita wa'adin karshe ga shugabannin Sudan ta Kudu har zuwa ranar 16 ga wannan wata na Oktoba da muke ciki. Wannan jan kafa dai da jinkiri da ake samu wata alama ce da ke nuna gazawar kungiyar kasahen yankin na gabashin Afirka wacce ta kunshi kasashen Sudan ta Kudu, da Sudan, da Habasha wato Ethiophia, da Kenya, da Yuganda da kuma Somaliya.

Äthiopien Friedensverhandlungen über Südsudan in Addis Ababa
Taron tattaunawa kan rikicin Sudan ta Kudu a Adis Ababa babban birnin kasar HabashaHoto: ZACHARIAS ABUBEKER/AFP/Getty Images

Kwalliya ta gaza biyan kudin sabulu

Wadanna kasashe dai na ta kai gwauro suna kuma kai mari a kan sulhunta bangarorin biyu tun cikin watan Mayu na wannan shekara ta 2014 amma kuma ba tare da kwalliya ta biya kudin sabulu ba. Wolf Christian Paes shi ne shugaban wata cibiyar nazari da ke nan birnin Bonn na Tarayyar Jamus, ya kuma ce:

"A yanzu ba na tsamanin a kwai wani cikekken shiri na samar da zaman lafiya tsakanin shugaba Kiir da jagoran 'yan adawar Riek Machar domin warware rikicin, tattaunawar ma ba a yin ta da gaskiya domin haka babu wani kyakkyawan sakamako da za a iya samu."

Rikici bayan samun 'yanci

Bayan yaƙin neman 'yancin cin gashin kai da kasar ta yi ta faman yi har zuwa shekarun 2011, a shekarun 2013 rashin jituwa ya kunno kai tsakanin shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar wanda ya zarga da yunkurin yi masa juyin mulki abin da ya sa aka kama wasu da dama daga cikin magoya bayansa bayan an tsige shi daga mulkin tare da wasu mukarrabansa. Sama da mutane 1000 ne suka hallaka sakamakon wannan rikici yayin da wasu dubbai suka kaurace wa gidajensu baya ga matsalar yunwa da ta addabi al'ummar kasar.

Südsudan UNAMIS Camp Juba 23.12.2013
'Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu da rikici ya tilasatawa kauracewa gidajensu.Hoto: Reuters

Yunkurin sulhun ya ci tura a lokuta da dama saboda rashin fahimtar da aka samu tsakanin bangarorin biyu da ke gaba da juna wajen rabon iko. Shi dai Shugaba Salva Kiir ya ki a nada Firaministan wucin gadi daga bangaren 'yan tawaye da ke goyon bayan Riek Machar wanda zai jagoranci kasar har ya zuwa lokacin gudanar da zabe.