1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya za ta darajanta kowane addini na kasar

Zainab Mohammed Abubakar/ BSApril 27, 2016

Magabatan kasar Turkiyya sun jaddada cewa addini ba zai yi tasiri a sabon kundin tsarin mulkin kasar ba, sabanin bayanan kakakin majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/1Ide4
Türkei Ministerpräsident Recep Tayyip Erdogan bei Trauerfeier mit Imam im Hintergrund
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan tare da babban Limamin kasarHoto: picture-alliance/dpa/Okten

Dumbin masu zanga-zanga ne suka yi ta rera wakokin nuna adawa da kalaman kakakin majalisar dokikin kasar Turkiyya. A wannan makon ne dai Ismail Kahraman ya ce al'ummar musulmin kasar wadanda su ne mafi rinjaye, na bukatar kundin tsarin mulki mai nasaba da addini, batu da ke sabani da tafarkin sauyi da Turkiyyan ke ciki, duk da cewar ya ce wannan ra'ayinsa ne kawai.

Türkei Protest gegen Ismail Kahraman Ankara
Masu zanga-zanga a TurkiyyaHoto: Reuters

"Bai kamata ace addini bai yi tasiri a sabon kundin tsarin mulkin ba. Kasashe uku ne kawai ke da kundin tsarin mulki da bashi da nasaba da addini. Faransa da Ireland da Turkiyya. Kuma babu ko ambatonsa. Sai dai alkalai na fassara wannan batu yadda suke so. Hakan bai dace ba. Bai kamata kundin tsarin mulki ya kaucewa addini ba."

Su ma dai manyan 'yan adawan kasar da suka hade a gangamin nuna adawar, sun ce kamata ya yi ace kakakin majalisar ya kare manufofin kasar amma ba ya dauki bangare ba. Kamar yadda Mahmut Tanal na babbar jam'iyyar adawa ta Republican Peoples Party ya bayyana.

"Mun zo nan ne domin kare tsarin mulkin da bashi da alaka da addini. Kakakin majalisar dokoki ya ce a alakanta tsarin mulki da addini. Wannan batu shi ne ya kawo hadin kai tsakanin al'ummar kasa. Idan aka cire bangaren da baya da alaka da addini a kundin tsarin mulkin, rigingimu na addini da yake-yake zai barke, kamar yadda muke gani a yankin Gabas ta Tsakiya".

Türkisch Premierminister Ahmet Davutoglu
Firaministan Turkiyya Ahmet DavutogluHoto: Getty Images/D. Mouhtaropoulos

Jam'iyyar AKP na kokarin maye gurbin kundin tsarin mulkin na yanzu da ke aiki tun daga shekarun 1980 bayan juyin mulkin sojoji. A matsayin kakakin majalisa, Kahraman ne ke kulawa da sabon kundin da ake rubutawa. Shi ma dai da yake tsokaci, Shugaba Recep Tayyp Erdogan ya jaddada cewar, dole ne gwamnati ta daidaita lamuranta kan kowane addini .Ya ce Turkiyya kasa ce da ke tafiyar da lamuranta bisa martaba wa dukkan al'ummarta, don haka kalaman na kakakin majalisa, ra'ayinsa ne kawai a dangane da mahawar da ke gudana kan sabon kundin.