Sakkwato: Wayar da kai kan tazarar haihuwa
December 4, 2024Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta jihar Sakkwato da kungiyoyin lafiyar, sun soma gangamin wayar da kan dangane da muhimmancin tazarar haihuwar ta hanyar bayar da horon ga masu sayar da shayi a kan yadda za su yada bayanai ga masu zuwa shan shayi dangane da muhimmancin soma yin tazarar haihuwar. Wannan gangami ya kunshi kananan hukumomi 10, wadanda suka hada da Wamakko da Gwadabawa da Wurno da Bodinga da Silame da Tambuwal da Dange/Shuni da Sokoto ta Arewa da kuma Sokoto ta Kudu. Manufar yin hakan shi ne yadda wuraren masu sayar da shayi ke zaman majalisu na hirar jama'a da ake tattauna muhimman batutuwa, kuma idan suka samu horo a kan muhimmanci tsarin iyali ko tazarar haihuwa akwai yiyuwar a samu nasara ga abun da ake son cimma. A kokarin ganin shirin gangamin ya samu karbuwa an tattaro dukkanin masu ruwa da tsaki a cikin al'umma, domin su mara baya da bayar da gudunmawa mutane su daure su karbi wannan tsari na tazarar iyali. Binciken likitoci ya nunar da cewa kawar da kai da yin ko oho ga tsarin tazarar iyalin, na haifar da wasu matsaloli da kalubale ga rayuwar 'ya'ya mata. A yanzu dai Hukumar Lafiya a Matakin Farko ta jihar Sakkwato da kungiyoyin lafiyar na fatan wannan wayar da kai ga tsarin iyali, ya samu karbuwa har dai a yankunan karkara da mata suka fi wahala a yayin da suke dauke da juna biyu.