1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Miliyoyin yara aka gano suna bauta a duniya

Mohammad Nasiru Awal June 12, 2015

Duk da kudurorin kare hakin yara kanana da dokoki na daidaikun kasashe, har yanzu a fadin duniya akwai yara kimanin miliyan 144 'yan kasa da shekaru 15 da ke aiki don kula da kansu da kuma sauran dangi.

https://p.dw.com/p/1FgU7
Ghana Kinderarbeit in Goldmine EINSCHRÄNKUNG
Yara na aikin tace ma'adanai masu hadariHoto: Foto: J. Kippenberg/Human Rights Watch/dpa

Wannan wani hali ne na gaba kura baya siyaki sakamakon talauci da kuma ci da gumin yara. A'isha 'yar shekaru shida daga kasar Mali tana aiki a kasuwar kifi ta garin Gao, Santiago dan shekaru 10 yana girbar barkono a gonar iyayensa a kasar Ecuador. Wadannan dai na daga cikin miliyoyin yara kanana da ke kwadago a duniya baki daya, wanda Asusun taimakon yara na Majalisar Dinikin Duniya UNICEF ya tattara hotunansu a cikin wani kundi, suna kuma aiki duk da yarjeniyoyi na kasa da kasa kamar yarjejeniyar kare hakin yara ta Majalisar Dinkin Duniya da ta kungiyar kwagado ta kasa da kasa. Alkalumman UNICEF sun nunar cewa a cikin shekaru 15 da suka gabata yawan yara 'yan shekarun haihuwa tsakanin biyar zuwa 17 da ke aiki ya ragu da misali kashi daya cikin uku. Iris Stolz mai kula da sashen kare hakin yara a kungiyar taimakon yara ta Jamus wato Terre des Hommes ta ce matukar akwai matsanancin talauci to zai yi wuya a haramta kwadagon yara a duniya baki daya. Kungiyar da ke aiki a kasashe 33 tana kuma gudanar da aikace-aikace ga yara.

Zabin bauta ko kwana da yunwa

Ta ce: "An haramta kwadagon yara a ko ina amma har yanzu yara na aiki. Zabin da ya rage musu shi ne ko dai su mutu da yunwa ko kuma su nemi kudi da kansu."

UNICEF Kinderarbeit 2015
Yaro na noma da kananan shekaruHoto: UNICEF

Ta kara da cewa ba za a iya haramta gaba daya kowane nau'i na aikin yara ba tare da duba halin rayuwar yaran ba.

Ta ce: "Hakan ya dogara ga aikin da tsawon lokacin yin aikin da kuma yanayin gudanar da aikin. Idan kai tsaye aka haramta musu yin aiki, to manyan kamfanoni da ke bin dokoki iya gwargwado ba za su iya daukar yara aiki ba. To ke nan yaran za su fada hannun kananan kamfanoni masu ci da gumin yaran, inda babu albashi mai yawa aikin kuma ke da hatsarin gaske."

Da wuya a kawar da bautar da yara kafin badi

Shi ma Asusun UNICEF yana wa matsalar irin wannan kalo. Kusan dukkan kasashen duniya sun dauki alhakin haramta duk wani aiki mai hatsari ga yara kafin shekarar 2016. Amma ba za a cimma wannan buri kafin badin ba inji Ninja Charbonneau ta Asusun UNICEF a Jamus, ta ce da sauran tafiya kafin a kawo karshen kwadagon da yara ke yi don kula da kansu ko dangi.

UNICEF Kinderarbeit 2015
Yarinya da daukar ruwan da ya fi karfintaHoto: UNICEF

Ta ce: "Da farko dole mu amince cewa kwadagon yara a zahiri yake. Daidai yake da matsalar talauci, ba za ka iya kawar da shi daga yau zuwa gobe ba."