Za a saki Karim Wada daga gidan kaso
June 17, 2016Shi dai Karim Wade na tsare ne a gidan kaso fiye da shekaru uku, inda kuma a watan Maris na 2015 aka yanke masa hukunci na daurin shekaru shida a gidan kaso tare da cinsa tara ta Euro miliyan 210 bayan da kotu ta ce ta kamashi da laifin arzuta kansa da kudaden hukuma. A wannan makon ne dai shugaban kasar ya sake bai wa babban jagoran adinin Muslunci na Mourides Serigne Sidi Makhtar Mbacké tabbaci kan batun sakin na Karim Wade din.
Shugaban kasar ta Senegal Macky Sall ya bayyana wa jagororin adinin Muslunci na kasar cewa bai taba fatan ganin Karim Wade ya je gidan kaso ba, sai dai kuma tsari ne na tafiyar da kyaukyawan mulki da gwamnatinsa ta sa ma gaba.
Ana ganin sakin na Karim Wade a halin yanzu tamkar lashe amai ne na shugaban kasar a gaban jam'iyyar adawa ta PDS ko kuma tsoma baki na shugabannin addini masu fada a ji a kasar.
Ana zargin Karim Wade dan tsohon shugaban kasa Abdoulaye Wade da laifin samun dukiya da aka kiyasta wadda ta kai ta Euro miliyan 178, wanda kuma ya samu wannan dukiya ce lokacin da ya rike mukamin mai bai wa shugaban kasa shawara da kuma minista a lokacin mulkin mahaifinsa. Da dama na ganin idan har aka sallamo shi to jam'iyyarsa ta PDS za ta nemi da a wanke shi daga wannan zargi da ya sha karyatawa domin ta tsayar da shi a matsayin dan takararta a zaben shekara ta 2019 mai zuwa.