A Afirka ta Kudu wasu jama'ar sun soma kada kuri'a
May 28, 2024Talla
Masu kada kuri'a miliyan 27 ne aka yi rajista. Fiye da miliyan daya da rabi suka yi rajista don kada kuri'a da wuri a kwanaki biyu kafin zaben.Tun bayan zaben Nelson Mandela, jam'iyyar ta lashe dukkanin zabukan kasar da gagarumin rinjaye,To amma a wannan karon jam'iyyar ANC na fuskantar barazanar rasa rinjaye a majalisar dokokin kasar, inda take tsakanin kashi 40% zuwa 47%. a hasashen da wasu kafofi masu zaman kansu suka yi.