Afirka ta Kudu: Kalubalen jam'iyyar ANC
May 22, 2024Masu sharhi kan al'amuran yau da kullum dai na cewa, akwai yiwuwa jam'iyyar ANC ta bai wa jama'a mamaki ta hanyar fito da dabarun da za su ba ta damar yin nasara duk da hasashen kalubalen da za ta fuskanta ake yi. Wannan shi ne lokacin zabe mafi girma da 'yan Afirka ta Kudu suka fi zakuwar zuwa akwatun zabe, domin sake zabar shugabanni a cikin shekaru 30 da kasar ta kwashe tana kan gwadaben dimukuradiyya.
Karin bayani: Tattalin arzikin Afirka ta Kudu na jan kafa
Kuri'un jin ra'ayin jama'a da aka gudanar kan zaben na ranar 29 ga watan Mayu, na alamta cewa jam'iyya mai mulki ta ANC za ta rasa karfinta a gwamnatin kasar. Sai dai Steven Gruzd da ke zama jami'i a Cibiyar Nazarin Harkokin Kasashen Ketare a Afirka ta Kudun, na da ra'ayin cewa ba dole ne abin da kuri'un jin ra'ayin jama'ar ya nunar ya kasance daidai da zaben ba.
Abubuwan da ake fargabar za su iya karya lagon jam'iyyar ANC a zaben sun hadar da zargin rashin shugabanci na gari da gaza biya wa 'yan kasa bukatunsu, a tsawon shekarun da jam'iyyar ta kwashe tana mulkar kasar. A baya dai ana jinjina kokarin jam'iyyar ta ANC, saboda shugabancin marigayi Nelson Mandela da ya yi fa ma yaki da wariyar launin fata. Sai dai a cewar Tessa Dooms da ke sharhi kan al'amuran siyasa a kasar ba wai jam'iyyar ANC ce kadai ke fuskantar barazana a zaben ba, gaba daya salon mulkin dimukuradiyyar ne ke fuskantar kalubale.
Karin bayani: Majalisar dokokin Afirka ta Kudu ta sake zaber Ramsphosa
Dooms ta ce zabukan da suka gabata a baya a kasar ba sa biyan bukatun talakawa, lamarin da ya sanya jama'a da dama yanke kauna cewa tafarkin na dimukuradiyya zai iya cire musu kitse daga wuta. Yanzu za a zuba ido a ga yadda za ta kaya a rumfunan zabe tsakanin Shugaba Cyril Ramaphosa mai hankoron yin tazarce da jam'iyyun adawa, wadanda ke kartar kasa suka kuma lashi takobin karya lagon jam'iyyar da ta kwashe shekaru tana jan zarenta a siyasar Afirka ta Kudun.