Boakai na gaban Weah a zaben Laberiya
November 15, 2023Talla
Hukumar Zaben Laberiyan ta bayyana cewa sakamakon da suka samu kawo yanzu daga kaso 22 cikin 100 na kuri'un da aka kidaya daga mazabun kasar a zagaye na biyun, babban jagoran adawar Joseph Boakai ya samu sama da 50 cikin 100 na kuri'un yayin da Shugaba George Weah ke da sama da kaso 49 cikin 100. 'Yan takarar biyu da ke kan gaba dai, sun gaza samun kaso 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Oktobar da ya gabata.