Laberiya: Zagaye na biyu na zaben shugaban kasa
November 14, 2023Jama'ar kasar ta Laberiya na kada kuri'ar ce a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa domin tantancewa ko dai su danka ragama ga shugaba mai ci kuma tsohon zakaran kwallon kafa George Weah ya ci gaba a wa'adi na biyu duk da sarkakiyar da ta dabaibaye mulkinsa ko kuma su zabi tsohon mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai duk da yawan shekarunsa.
Ana sa ran zaben zai kasance kan-kan-kan tsakanin abokan hamaiyar biyu wadanda suka taba karawa a 2017 lokacin da Weah ya sami nasara a zagaye na biyu da fiye da kashi 61 cikin dari na kuri'un da aka kada.
A zagayen farko na zaben da aka yi a ranar 10 ga watan Oktoba Weah mai shekaru 58 da Boakai mai shekaru 78 sun yi kusan kunnen doki da fiye da kashi 43 cikin dari na kuri'un.
Mutane fiye da miliyan biyu da dubu dari hudu suka yi rajistar kada kuri'a.
Shugaba mai ci na da farin jini musamman wajen matasa, sai dai kuma sai ya dage wajen kare gwamnatinsa.
A daya bangaren kuma Boakai wanda tsohon hannu ne ya rike mukamai da dama a gwamnati da kuma fannin kasuwanci.
Hukumar zaben dai na da kwanaki 15 ta baiyana sakamakon zaben ko kuma kasa da haka a cewar wani jami'in zaben Samuel Cole.