Zaɓen shugaban ƙasar Angola
August 30, 2012Yaƙin neman zaɓe a Angola ya kasance tamkar abinda malam bahaushe ke dangatawa da "gamin ƙwai da duste". A nan dutsen jam'iyar MPLA ce, wadda ke kan mulki tun samun 'yancin kan Angola a shekara 1975, da kuma shugabanta Jose Eduardo dos Santos, wanda ya share shekaru 33 ya na mulkin ƙasar, kuma yake buƙatar yin tazarce.
A jawabin ƙarshe da yai lokacin kammalla yaƙin neman zaɓe dos Santos cewa ya yi:
" ƙasarmu ta kama ingattatar hanyar cigaba, saboda haka wajibi ne mu cigaba da ƙoƙarin da muka faro na kyautata rayuwar 'yan ƙasa da kuma haɓɓaka tattalin arziki, a daidai wannan lokaci, ba za mu saki ƙasa ba ga hannun 'yan adawa 'yan dagaji."
Dos Santos na daga sahun shugabanin Afrika irin su Robert Mugabe na Zimbabwe, da Teodoro Obiang na Equatorial Guinea, da suka jima suna karyawa inda babu gaɓa a tafiyar da harkokin mulkin ƙasashensu.
A cewar Rafael Marques wani ɗan jarida a ƙasar Angola,a wannan karo ma ko shakka babu, ta ko wane hali shugaba dos Santos zai yi tazarce, domin babu wata adawa mai ƙarfi da za ta iya taka masa birki.Shi kansa ɗan takara jam'iyar adawa ta UNITA Isaias Samakuva da ya gaji Jonas Savimbi ba shi da ƙarfin zuciyar ƙalubalantar dos Santos, daɗa balle uwa uba Abel Chivukuvuku ɗan takara jam'iyar Casa-CE da ta ɓalle daga UNITA:
"Dangane da yadda a ka tsara zaɓen ko shakka babu jam'iya mai mulki za ta lashe shi, domin an tanadi hanyoyin maguɗi da dama.Misali daga cikin mutane miliyan Tara da ya cencenta su yi zaɓe, miliyan shida ba su da katocin zaɓe, bugu da ƙari katocin zaɓe miliyan ɗaya da rabi na cikin hannuwan hukumomin a matakai daban-daban na jam'iyar MPLA.Sannan wata matsalar ma itace,daga 'yan ƙwarorin mutanen da su samu damar yin zaɓen mafi yawa ba su san runfuna da za su kaɗa ƙuri'a ba.Kai kar in kai ka nesa, babu mutumen Angola ɗaya da ke da shakku game da sakamakon wannan zaɓe".
Suma ƙungiyoyin kare haƙƙoƙin bani Adama sun yi ƙorafi game da matakan shirya maguɗi da gwamnatin Angola ta ɗauka a wannan zaɓe, kamar yadda Lisa Rimli wata 'yar ƙasar Angola dake aiki a ƙungiyar Human Rights Wach:
"Saban zaɓen shekara bana, a zaɓen shekara 2008 an samu babbar tawagar ƙungiyar tarayya Turai wadda ta sa ido a zaɓen Angola.
A wannan karo ƙalilan ne daga masu sa idon suka samu takardun izinin shiga ƙasar.Sannan zaɓen zai wakana cikin mummunan yanayin take haƙƙoƙin faɗin albarkcin bakin jama'a da na walwala."
Isaias Samakuva,ɗan takara babbar jam'iyar adawa ta UNITA, yayi ƙorafin maguɗi , saboda haka ne ma ya gayyaci wani babban taron gangamin magoya bayansa, to amma wannan mataki na tsayin ihunka banza, kamar yadda ya baiyana:
"Dalili da matakai iri-iri na maguɗi da mu ka bankaɗo mun bukaci a ɗage zaɓen amma gwamnati ta yi kunnen uwar shegu.Mun bada shawara a ɗaga shi ko da wata guda,amma ba a saurare mu ba."
Babu tababa, shugaba Jose Eduardo dos Santos za shi tazarce a wannan zaɓe, to saidai a ayara tambaya itace wane martani gamayyar kasa da ƙasa za ta maidawa a daidai wannan lokaci da ake gwagwarmayar shimfiɗa tsaftacen tsarin demokraɗiya a ƙasashen duniya.
Mawallafi:Antonio/ Yahouza
Edita Umaru Aliyu